Labarai
Najeriya da Qatar Sun Cimma Yarjejeniyoyin Hadin Gwiwa
Shugaban kasa Bola Tinubu da sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, sun sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi da za su bude kofar inganta muhimman fannoni tsakanin kasashen biyu.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya ce an cimma yarjejeniyar ce a fadar sarkin Qatar.
Yace bangaren da yarjejeniyoyin za su shafa sun hadar da fannonin ilimi da kasuwanci da inganta zuba jari, da sama wa matasa ayyuka da harkar ma’adinai da yawan bude ido da wasanni.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce a shirye kasarsa take don yin maraba da masu zuba jari, yana mai cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi na inganta zuba jari a kasar.
Ya ce babban karfinmu shi ne mutanenmu. karfinmu ya dogara kan matasanmu. suna da karfi , da fikira da yarda da kansu,” in ji shugaban na Najeriya.
Ya kara da cewa matasan kasar na da ilimi kuma suna da fikirar neman sana’a a duk inda take.
Shugaba Tinubu ya nada ministan kudi da na tattalin arziki, mista Wale Edun a matsayin wanda zai jagoranci tawagar gwamnatin Najeriya da za ta tattauna da hukumomin Qatar wajen gano bangarorin da za a zuba jarin da aiwatar da shi, don ciyar da kasar gaba.
Shugaba Tinubu dai na ziyarar aiki a kasar Qatar tare da wasu manyan jami’an gwamnatinsa.
- Bello Wakili
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
