Connect with us

Labarai

Manyan Attajiran Duniya Sun Halarci Bikin Auren Dan Wani Attajiri A Indiya

Published

on

Wasu daga cikin manyan masu fada a ji a duniya sun isa jihar Gujarat ta kasar Indiya domin halartar bikin auren mutum mafi dukiya a nahiyar Asiya.

 

Daga cikin bakin akwai shugaban facebook Mark Zuckerberg da shahararriyar mawakiya Rihanna da tsohon wanda ya fi kowa arziki a duniya Bill Gates.

 

Dukkanin su sun halarci walimar da Mukesh Ambani, shugaban rukunin kamfanonin Reliance Industries, kuma attajiri mafi dukiya a nahiyar Asiya ya shirya domin murnan bikin auren dan shi.

 

Matashi Anant Ambani, mai shekara 28 a duniya zai auri masoyiyarsa Radhika Merchant a cikin watan Yuli.

Shahararrun ‘yan wasan fina finan  Indiya, Shah Rukh Khan da Amitabh Bachchan na daga cikin wadanda suka halarci walimar ta kwana uku wadda ta gudana a birnin Jamnagar.

 

Yanzu haka Mukesh Ambani, mai shekara 66 a duniya shi ne mutum na 10 a jerin mutane mafiya kudi a duniya, inda dukiyarsa ta kai dalar Amurka biliyan 115, kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.

 

Mahaifin Mukeh Ambani ne ya kafa rukunin kamfanin Reliance Industries a shekarar 1966, wanda katafaren rukunin kamfanoni ne da ya kunshi hadawa da sayar da kaya daban-daban sai kuma harkar hada-hadar kudi da na sadarwa.

 

Anant Ambani shi ne dan’auta a cikin ‘yayan mahaifin nasa uku, wadanda dukkanin su suke cikin manyan shugabannin rukunin kamfanonin na Reliance Industries.

Matashin na aiki a bangaren kasuwancin makamashi na rukunin kamfanonin kuma yana cikin shugabannin da ke tafiyar da lamurran gidauniyar rukunin kamfanonin.

 

Wannan kasaitacciyar walimar aure ta ji da gani daya ce daga cikin irin su da iyalan na Ambani suka yi kaurin suna wajen shiryawa.

A shekarar 2018, shahararriyar mawakiyar Amurka, Beyonce na daga cikin wadanda suka cashe a walimar daurin auren ‘yar Mista Ambani, Isha Ambani, wanda aka yi a birnin Udaipur. Tsofaffin sakatarorin harkokin waje na Amurka Hillary Clinton da John Kerry na daga cikin wadanda suka halarci walimar ta wancan lokaci.

 

Wani rahoto na kafar yada labaru ta Bloomberg a wancan lokaci ya kiyasta cewa an kashe kudi dalar Amurka miliyan 100 a lokacin bikin – sai dai wani ‘na kusa da iyalin Ambani’ ya musanta batun, inda ya ce kudin da aka kashe bai wuce dala miliyan 15 ba.

 

Walimar ta wannan karo ta fara ne daga farkon wannan mako, inda iyalin na Ambani suka raba abinci ga al’ummar garin Jamnagar.

Sauran bakin da aka gani wurin taron sun hada da maidakin tsohon shugaban Amurka, Ivanka Trump, da tsoffin firaministocin Canada da Autralia, wato Stephen Harper da Kevin Rudd.

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Fasaha2 hours ago

Gwamnan Kaduna Ya Kaddamar Da Sabbin Ajujuwa A Zaria

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya kaddamar da rukunin ajujuwa 18 a makarantun Basic Education guda biyu dake karamar hukumar...

Fasaha2 hours ago

Shugaban Kasa Ya Kaddamar Sabon Birnin Kasuwanci A Abuja

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da samarda wani da za a samar don gudanarda harkokin kasuwanci a cikinsa da...

Labarai3 hours ago

Kungiyar CAN Ta Rasa Mata Shida A Hadarin Mota A Taraba

An bayyana cewa wasu ’yan kungiyar mata ta kungiyar Kiristoci ta Najeriya (WOWICAN) su shida ne suka rasa rayukansu a...

Labarai3 hours ago

‘Yan Sakai Jihar Taraba Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa

Rundunar ‘yan banga ta Najeriya (VGN) reshen jihar Taraba ta yi nasarar ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa...

Ilimi3 hours ago

Talatar Nan Jirgin farko na Maniyatan jihar Kwara Zai Tashi

An dage tashin jirgin farko daga filin jirgin sama na Janar Tunde Idiagbon na kasa da kasa na Ilorin don...

Labarai3 hours ago

HARIN MASALLACIN KANO: Obi Ya Ziyarci Wadanda suka Mutu

  Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP) a zaben 2023, Peter Obi, ya ziyarci wadanda kona masallacin Kano...

Labarai4 hours ago

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi Ta Yi Kiran A Yiwa Mijinta Addu’a

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Zainab Nasir Idris, ta ce addu’a ita ce ginshikin duk wani shugabanci mai nasara, don...

Labarai4 hours ago

Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitin Kwanar Ganduje A Kano

Gwamnatin jihar Kano, ta rufe tare asibitin Kwanar Ganduje dake unguwar Sharada Karamar Hukumar Kano Municipal.   Babban daraktan hukumar...

Labarai4 hours ago

Shugaban Iran Ebrahim Raisi Ya Rasu A Hatsarin Jirgi

Jami’an Iran sun ce Shugaba Ebrahim Raisi da ministan harkokin wajen ƙasar, Hossein Amir-Abdollahian sun rasu a wani hatsarin jirgin...

Labarai15 hours ago

Ma’aikatan Ceto Na Cigaba Da Neman Jirgin Shugaban Kasar Iran Da Ya Bace

Da yammacin yau lahadi ne tarin ma’aikatan ceto suka bazama wajen aiki gano jirgi mai saukar ungulu dauke da shugaba...

Mafi Shahara