Labarai
‘Yan Sakai Jihar Taraba Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Yi Garkuwa

Rundunar ‘yan banga ta Najeriya (VGN) reshen jihar Taraba ta yi nasarar ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su.
Kakakin rundunar, Suleiman Aliyu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Jalingo.
An ceto wadanda lamarin ya rutsa da su ne a lokacin da jami’an tsaro na musamman na VGN suka mamaye sansanonin masu garkuwa da mutane a tsaunin Kachalla da ke cikin karamar hukumar Lau ta jihar bayan samun labarin.
Wadanda aka ceto sun hada da Alhaji Dankawu mai shekaru 60 da haihuwa da Haruna Shagari mai shekaru 13 da kuma Alhaji Isa mai shekaru 67.
An yi garkuwa da Alhaji Dankawu a Garin Dogo, Haruna Shagari a Yolde Kindang, da Alhaji Isa a kauyen Lushi. Daya daga cikin wadanda harin ya rutsa da su Haruna Shagari ya koma ga iyalansa.
A yayin samamen, rundunar ta cafke biyu daga cikin wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane, Sale Manu da Manu Siddiki, wadanda suka amsa laifinsu ba tare da azabtar da su ba.
A cikin wani faifan bidiyo, Sale Manu ya bayyana musamman cewa sun mallaki bindigu kirar AK47 guda biyar (5) domin gudanar da aiki tare da lissafta wasu ‘yan kungiyar da ke gudun hijira a halin yanzu.
Kwamandan VGN, Munir Bello Abubakar, wanda shi ne mataimakin kwamandan mulki na shiyyar arewa maso gabas, ya bayyana cewa sun lalata sansanonin masu garkuwa da mutane a tsaunin Kachalla dake karamar hukumar Lau ta jihar a ranar 12 ga watan Mayu, 2024.
Bugu da kari, wani dan infoma mai suna Murtala Santi, wanda ke zaune a Minda kan hanyar Kona-Lau, shi ma ya shiga hannun ‘Yan bangar.
Kwamanda Munir Bello Abubakar ya jaddada aniyar su na ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro wajen yaki da miyagun laifuka a fadin jihar.
Sani Sulaiman/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
