Connect with us

Labarai

Majalisar Wakilai Za Ta Gabatar Da Dokoki Biyar Don Gyara Bangaren Man Fetur

Published

on

Majalisar Wakilai za ta gabatar da kudurori guda biyar da za su magance manyan kalubale da ke hana ingantaccen aiki a harkar man fetur ta kasa.

Shugaban kwamitin Majalisar kan Albarkatun Man Fetur, Alhaji Alhassan Ado Doguwa, ne ya bayyana hakan yayin wani taro na hadin gwiwa da kwamitin musamman kan matsalar satar danyen mai a Abuja.

Alhaji Alhassan Ado Doguwa ya ce kudurorin da ake shirin gabatarwa, za a gabatar da su ne tare da shugabannin kwamitocin biyu, kuma wani bangare ne na matakan dokoki don tallafawa kokarin gwamnati wajen kare kadarorin man fetur da gas da kuma dakile matsalar satar danyen mai.

Ya bayyana cewa daya daga cikin kudurorin na neman kafa Hukumar Kasa da za ta sami ikon dakile ayyukan  masu lalata bututun mai da gurfanar da su , da kuma aikata wasu laifuka da suka shafi bangaren man fetur.

Kwamitocin da duk Majalisar baki daya na matukar damuwa da karuwar rashin tsaro da ayyukan laifi a yankunan da ake hakar mai. Wannan mataki na majalisa wata hanya ce ta tallafa wa kokarin gwamnati wajen kare wadannan muhimman kadarorin kasa,” in ji Alhaji Ado Doguwa.

Har ila yau, Alhaji Ado Doguwa ya bayyana cewa daya daga cikin kudurorin da ke karkashin Kwamitin Albarkatun Man Fetur (Sashen Sama), wanda Kakakin Majalisar, Dr Abbas Tajuddeen, ke jagoranta, na neman kafa Hukumar da za ta kula da cire kayan aikin hakar mai da suka tsufa, matsala da ke da matukar muhimmanci ga al’ummomin da ke karbar bakuncin ayyukan man fetur da sauran masu ruwa da tsaki.

 

Salihu Tsibiri 

Labarai

Labarai18 hours ago

Ana Zargin Mutum 140 Sun Bace Bayan Nutsewar Jirgin Ruwan Iran a Gaɓar Sri Lanka

Rundunar sojin ruwan Sri Lanka ta tabbatar da ceto mutum 32 bayan samun kiran gaggawa daga jirgin ruwan sojin Iran...

Ilimi18 hours ago

Gwamnatin Tarayya da ke Gusau za ta Kafa Cibiyar Nazari kan Tarihi da Al’adun Zamfara

Daga Aminu Dalhatu  Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Gusau (FUGUS), Farfesa Tukur Adamu, ya sanar da shirin jami’ar na kafa...

Labarai19 hours ago

Jam’iyyar APC Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni a Jihar Kano

Daga Abdullahi Jalaluddeen Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Kano ta zaɓi sabbin shugabanni domin jagorantar harkokin jam’iyyar. Zaɓen,...

Labarai20 hours ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Miliyoyin Naira Don Sayen Gidaje 96 Daga Gwamnatin Tarayya

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Miliyan 853 domin sayen gidaje guda...

Labarai2 days ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai3 days ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai3 days ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai3 days ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Mafi Shahara