Connect with us

Labarai

Majalisar Jigawa Ta Bukaci Kananan Hukumomi Su Gabatar da Kasafin Kudinsu a Zangon Farko na Sabuwar Shekara

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Shugaban kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Aminu Zakari, ya bukaci ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar  tabbatar da ganin cewa kananan hukumonin jihar 27 sun wallafa cikakken kundin kasafin kudadensu cikin zangon farko na sabuwar shekara.

Alhaji Aminu Zakari wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa, ya bayyana haka ne lokacin tantance kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara na ma’aikatar kananan hukumomi.

Ya kuma yi kira ga ma’aikatar da ta duba batun rashin biyan albashi ga wasu daga cikin nadaddun kansiloli, kasancewar yanzu haka akwai nadaddun kansiloli 21 da ba sa samun albashin su.

Ya kara da cewar, kwamitin ya samu koke kan tsallake albashin wasu ma’aikatan kananan hukumomi sakamakon aikin tantance ma’aikata na IPPS  ta yadda wasu ma’aikatan sun yi ritaya ba tare sun karbi albashin da aka tsallake su ba.

A nasa jawabin, kwamishinan ma’aikatar kananan hikumomin Jihar, Alhaji Ibrahim Garba Hannun Giwa, ya bada tabbacin yin duk abinda ya kamata domin magance wadannan batutuwa.

Ya ce ma’aikatar ta yi kiyasin kashe naira miliyan dubu 13 domin gudanar da manyan ayyuka da harkokin yau da kullum a shekarar 2026.

Hannun Giwa, ya kuma bayyana cewar daga cikin manyan ayyuka akwai gyaran ofisoshin shiyya na jami’an duba kananan hukumomi guda 7.

Yana mai cewar za’a kuma kammala aikin ginin sabbin ofisoshi dake kananan hukumomin Babura da Kafin Hausa.

Kazalika, Kwamishinan ya ce za’a sayi motocin aiki da babura ga jami’an duba kananan hukimomi da mataimakansu, tare da kudaden gudanarwa domin ziyarar aiki a lungu da sakon kananan hukumomin jihar 27.

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara