Connect with us

Labarai

Shugaban Majalisar Wakilai Dr. Abbas ya Tallafawa Aikin Raya Kasa da Ake Yi a Lere da Naira Miliyan 5

Published

on

Shugaban Majalisar Wakilai ya jadda da kudurin Majalisar Dokokin Kasa na tallafawa Kungiyoyin raya al’umma.

Shugaban Majalisar Wakilai Dr. Tajuddeen Abbas, ya jadda da kudurin Majalisar Dokokin Kasa wajen tallafawa ayyukan da Kungiyoyin raya al’umma suka aiwatar a fadin Kasar Nan.

Dr. Tajuddeen Abbas ya ambata haka ne, lokacin taron kaddamar da kalandar (ALMANAC) na Kungiyar raya garin Lere watau Lere Development Association (LDA) na shekara ta 2026, Wanda aka Yi a Lere ta Jihar Kaduna.

Kakakin Majalisar Wanda Hon. Alhassan Ado Doguwa ya wakilci shi a wajen taron, ya ce Majalisar Dokokin Kasa ta himmatu wajen yin Dokoki da zasu baiwa Kungiyoyi damar aiwatar da ayyukan Kawu cigaba ga al’ummominsu.

Ya Yi bayanin cewa, Gwamnati Mai ci tana aiki kafada da kafada da al’ummomin Kasar Nan wajen maido da zaman Lafiya da tsaro a Kasa.

Dr. Tajuddeen Abbas ya karfafa guiwar Kungiyar ta Lere Development Association LDA ta cigaba da tallafawa kokarin Gwamnati wajen aiwatar da manufofinta da suka shafi rayuwar Yan Nigeria Kai Tsaye.

Kazalika, Shugaban Majalisar ya baiwa Kungiyar ta raya garin Lere gudunmawar Naira Miliyan Biyar domin cigaba da gudanar da hidimominta.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Karamar Hukumar LERE, Alhaji Jafar Ahmed ya bukaci Kungiyoyin raya al’umma su kirkiro shirye shiryen da zasu taimakawa Gwamnati wajen samar da guraban aikin yi ga Matasa.

Ya yabawa Kungiyar LERE Development Association LDA bisa yadda take Jan ragamar aiwatar da ayyukan raya Kasa a yankin.

Tun farko sai da Mai Martaba Sarkin LERE, Engr. Sulaiman Umaru, ya bayyana godiyarsa bisa yadda Shugaban Majalisar yake taimakawa al’ummomin Kasar Nan.

An gudanar da raye rayen al’adun gargajiya a wajen taron Wanda ya Sami halartan mashahuran Yan Nigeria.

COV/Sani Lere

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara