Labarai
Hajjin 2026: An Nada Sarkin Dutse Amirul Hajj na Jihar Jigawa
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamna Umar ya naɗa Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Muhammadu Sanusi a matsayin Amirul Hajj na jihar domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Alhaji Habibu Yusuf Adamu ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a hedikwatar hukumar da ke Dutse.

Ya ce an naɗa Sarkin a matsayin Amirul Hajj kuma jagoran tawagar gwamnati tare da wasu mambobi huɗu domin gudanar da aikin Hajjin 2026 a ƙasa mai tsarki.
Habibu ya ce mambobin huɗun sun haɗa da Kachallan Dutse, Alhaji Kabiru Ali, Malam Umaru Nassarawa, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Kazaure, Imam Salisu Abubakar, da kuma wakilin Sarkin Gumel.
Jami’in ya ƙara da cewa, dukkan naɗe-naɗen sun fara aiki nan take.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
