Labarai
Jigawa: Hukumar Alhazai ta Yaba da Naɗin Sarkin Dutse Amirul Hajjin 2026
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa naɗa Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Muhammadu Sanusi a matsayin jagoran Alhazan jihar a aikin Hajjin shekarar 2026.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Alhaji Habibu Yusuf Adamu, ya fitar ga manema labarai a Dutse.
Ya bayyana cewa, Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya ce naɗin ya dace ƙwarai, la’akari da jajircewar Sarkin wajen harkokin addini da kuma rawar da yake takawa a matsayin babban jagoran al’umma a Jihar Jigawa.
Ahmed Labbo ya jaddada cewa Amirul Hajj na shekarar 2026 yana da cikakken ilimin addini da ya dace domin jagorantar tawagar jihar.
Ya kuma yi alƙawarin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da Amirul Hajjin, tare da neman shawararsa a matsayin jagoran al’umma kan duk wasu lamurra da za su taso yayin gudanar da aikin.
Darakta Janar ɗin, a madadin ma’aikatan hukumar, ya miƙa saƙon taya murna ga Amirul Hajji, tare da tabbatar da aniyar ma’aikatansa na yin aiki tare.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya naɗa Sarkin Dutse a matsayin Amirul Hajj domin jagorantar Alhazan jihar zuwa ƙasar Saudiyya a aikin Hajjin shekarar 2026.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
