Labarai
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta Amince da Kudirin Kasafin 2026
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta amince da Kudirin Dokar Kasafin Kuɗin shekarar 2026 na sama da naira biliyan 901, tare da sanya hannu ya zama doka, bayan yin wasu gyare-gyare.
Wannan ya biyo bayan gabatarwa da kuma amincewa da rahoton Kwamitin Majalisar kan Kasafin Kuɗi.
Yayin gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin wanda ke wakiltar Mazabar Malam Madori, Alhaji Hamza Adamu Ibrahim, ya bayyana cewa dukkan Kwamitocin Majalisar sun tattauna da Ma’aikatun Gwamnati da Hukumominsu kan tantancewa da kare ƙididdigar kasafin kuɗinsu.
Ya ce duba da abubuwan da kasafin ya ƙunsa, kwamitin ya gamsu da rabon kuɗaɗen da aka ware domin samar da ababen more rayuwa da walwalar al’umma a shekarar kasafin kuɗin 2026.
Dangane da kasafin kuɗin ƙananan hukumomi 27 da ya haura naira biliyan 288, Hamza Adamu ya yi kira ga Ma’aikatar Kananan Hukumomi da ta tabbatar cewa shugabannin ƙananan hukumomi suna bin aiwatar da kasafin kuɗinsu yadda ya dace domin jin daɗin al’ummar karkara.
A yayin zaman Kwamitin Majalisa gaba ɗaya (Committee of the Whole), Shugaban Majalisar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin, ya karɓa tare da duba shawarwari da gyare-gyare kan kura-kurai na rubutu musamman sunayen garuruwa da wurare.
Da aka koma zaman Majalisa na gaba ɗaya, Mataimakin Magatakardar Majalisa, Alhaji Yusha’u Muhammad, ya karanta kudirin dokar karo na biyu da na uku, inda Shugaban Majalisar, Haruna Aliyu Dangyatin, ya sanar da amincewa da Kudirin Dokar Kasafin Kuɗin shekarar 2026 ya zama doka.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
