Labarai
Mun Ƙarfafa Tsaron Makarantu da Kadarorin Gwamnati a Jihar Jigawa- NSCDC
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Kasa (NSCDC) ta yi bitar ayyukanta na shekarar 2025 a Jihar Jigawa, inda ta bayyana manyan nasarori da ta samu a fannin tsaro da kare muhimman kayayyakin gwamnati.
Kwamandan NSCDC na Jihar Jigawa, Muhammad Kabir Ingawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse yayin da yake bitar ayyukan hukumar na shekarar 2025.
Dangane da gurfanar da masu laifi, Ingawa ya ce hukumar ta yi nasarar gurfanar masu laifuka 125 a gaban kotu.
A cewarsa, shari’o’in sun haɗa da laifukan lalata dukiyar jama’a, laifukan damfara ta yanar gizo, yin sojan gona da sauran laifukan da suka shafi tsaro.
Shugaban NSCDC ya ce an kama waɗanda ake zargi da lalata kayan wutar lantarki da cibiyoyin ruwa, inda darajar kayayyakin da aka lalata ta haura naira miliyan 11.
A ƙarƙashin shirin School Safe Initiative, ya ce NSCDC ta samar da tsaro ga makarantu a faɗin jihar, tare da horar da jami’an da aka tura wannan shiri domin ƙara tabbatar da tsaro a makarantu a shekarar da ake bita.
Kwamandan NSCDC ya gode wa Gwamnatin Jihar Jigawa bisa bayar da motocin aiki guda uku, tare da sauran tallafin da aka samu daga masu ruwa da tsaki a faɗin jihar.
Muhammad Ingawa ya ce ya kara da cewa an kafa cibiyar sa ido ta zamani wacce a halin ake gwajin ayyukanta.
Ya ce cibiyar za ta tattara bayanan dukkan makarantu da ke ƙarƙashin shirin, tare da tabbatar da sa ido na awanni 24 domin ingantaccen tsaro da kulawa da ayyukan makarantu.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
