Labarai
Katin Zabe: PDP Ta Bukaci Mambobinta Su Hanzarta Yin Rajista
Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kwara, ta bukaci magoya bayanta da ’yan jam’iyya a gida da waje su yi amfani da damar da Hukumar ZabjaMai Zaman Kantdata Kasa (INEC) ta bada na ci gaba da yin rajistar masu kada kuri’a (CVR) domin sabbin mambobi su yi rajista.
A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam’iyyar a jihar, Olusegun Adewara, ya fitar, ya ce ya zama wajibi ga ’yan jam’iyyar PDP a fadin jihar, musamman manyan masu ruwa da tsaki, jami’an jam’iyya da masu neman takarar mukamai daban-daban, su dauki wannan rajista a matsayin babban aiki a mazabunsu.
Sanarwar ta bayyana cewa wannan rajista na daga cikin muhimman ginshikan fafutukar #RescueKwara (Ceto Jihar Kwara) da jam’iyyar ke yi domin zaben 2027.
Haka kuma sanarwar ta yi kira ga mambobin jam’iyyar da su bai wa wannan tsari fifiko, tare da mallakar katin zabe, wanda shi ne zai basu damar kada kuri’a a zabukan 2027.
“Muna tunatar da mambobinmu cewa katin zabe na dindindin (PVC) da INEC ke bayarwa shi ne kadai sahihin abu da masu kada kuri’a za su yi amfani da shi wajen gyara halin rashin tsaro, talauci da rashin shugabanci na gaskiya da ke damun jihar Kwara tun daga 2019,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma bukaci mambobi, musamman masu ruwa da tsaki a jam’iyyar, jami’ai da masu neman mukaman siyasa daban-daban, da su tabbatar da bin wannan umarni a mazabunsu domin tabbatar da karfin jam’iyyar.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
