Labarai
Gobara Ta Kona Shaguna 22 A Kasuwar Kara Da Ke Kwara
Wuta da ta tashi da sanyin safiya ta kona shaguna 22 da kwantena 6 a kasuwar Kara, da ke Ajase-Ipo, karamar hukumar Irepodun ta jihar Kwara.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Hassan Adekunle, ya fitar, ya bayyana cewa gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe daya da rabi na dare.
A cewarsa, lokacin da jami’an kashe gobara suka isa wurin, sun gano cewa daga cikin shaguna 323 da ke kasuwar, ciki har da shagunan katako 22 da rumfunan ƙarfe 7.
Binciken farko ya nuna cewa sakaci ne ya jawo lamarin, inda wani daga cikin masu shagunan katako ya yi girki ba tare da ya kashe wutar da kyau ba, wanda daga bisani ta sake ruruwa ta bazu zuwa shaguna na kusa.

Sanarwar ta ce saurin kai dauki da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara ta yi ne ya hana gobarar bazuwa zuwa sauran wurare, inda hakan ya ceci daruruwan shaguna da kadarori daga lalacewa.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara ya yi kira ga jama’a da su rika kula wajen mu’amala da wuta, tare da daukar matakan kariya da muhimmanci, musamman a kasuwannin da ake da kayayyakin da ke iya kamawa da wuta cikin sauki.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
