Labarai
Gwamna Yusuf Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe Ta Jihar Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da Barista Sa’idu Yahaya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC).
An gudanar da wannan gajeren bikin ne a gidan gwamnati na Kano, inda Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari’a na jihar, Barista Haruna Isa Dederi, ya jagoranci rantsar da shi.
Idan za a tuna Gwamna Yusuf ya gabatar da sunan Sa’idu Yahaya ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin tantancewa da tabbatarwa bisa tsarin doka, inda daga bisani majalisar ta amince da nadin nasa.
Barista Sa’idu Yahaya ƙwararren masani ne a fannin yaƙi da cin hanci, wanda ya goge a aikinsa shekaru sama da 18. Ya yi aiki a Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Sauran Laifuka Masu Alaƙa (ICPC), inda ya kware a bincike, da gano kadarori.
Da yake taya shi murna, Gwamna Yusuf ya nuna kwarin gwiwa cewa Yahaya zai sake fasalta PCACC tare da ƙarfafa jajircewar gwamnatin jihar wajen yaƙar cin hanci da wanzar da gaskiya a cikin mulki.
Ya yi kira a gare shi da ya gudanar da aikinsa bisa gaskiya da adalci, inda ya ƙara jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tsayawa kan gaskiya da riƙon amana a hidimar jama’a.
A jawabinsa bayan an rantsar da shi, Barista Yahaya ya yi alƙawarin tabbatar da amincewar da aka nuna gare shi, inda ya ce zai ƙara kaimi wajen rage cin hanci, dawo da kadarorin da aka wawure, da tabbatar da adalci ga dukkan jama’ar Kano.
Hukumar PCACC, wacce aka kafa domin karɓar ƙorafe-ƙorafen jama’a da kuma yaƙar cin hanci a matakin jiha, ana sa ran za ta taka muhimmiyar rawa a ƙarƙashin shugabancin Sa’idu Yahaya wajen cike gibin da hukumomin tarayya suka bari.
Abdullahi Jalaluddeen
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
