Labarai
Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya ta Rantsar da Sabon Shugabanta a Gusau
Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen Jihar Zamfara, ta rantsar da Surajo Garba Gusau a matsayin sabon shugabanta.
Babbar Mai Shari’a ta Jihar Zamfara, Mai Shari’a Kulu Aliyu, ce ta jagoranci rantsar da sabon shugaban a wajen bikin da aka gudanar a Gusau.

A jawabin sa na farko, Surajo Garba Gusau ya bayyana wannan rana a matsayin muhimmin tarihi a ci gaban ƙungiyar a Jihar Zamfara.
Ya yabawa jajircewar shugabannin da suka gabata wajen bunƙasa harkokin aikin lauya a jihar, tare da yin alƙawarin kara zage dantse kan nasarorin da suka bari.
Sai dai, sabon sshugabanna NBA ya nuna damuwarsa kan rashin samun sakatariyar kungiyar a Gusau, wanda ya ce hakan yana jawo cikas wajen gudanar da harkokin ƙungiyar.
Barista Surajo Garba ya tabbatar da cewa shugabancinsa zai yi aiki tare da hukumomin gwamnati, kungiyoyin fararen hula, masu hannu da shuni da kuma abokan hulɗar ƙasa da ƙasa, domin samar da sakatariyar ga ƙungiyar.

A sakonsa na taya murna, Kwamishinan Shari’a na Jihar Zamfara ya taya sabon shugabanci murna, inda ya bayyana rantsarwar a matsayin babban tarihi.
Ya bayyana kwarin gwiwa cewa sabon shugaban zai iya sauya fasalin ƙungiyar, tare da yin kira gare shi da ya kasance mai jajircewa, da gaskiya wajen ci gaba da gyare-gyare don bunƙasar NBA a jihar.
Daga Aminu Dalhatu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
