Connect with us

Labarai

Karamar Hukumar Gwarzo Ta Raba Magunguna Da Kayan Aiki Ga Asibitoci

Published

on

A yunƙurinta na inganta harkar kiwon lafiya, Karamar Hukumar Gwarzo ta raba muhimman magunguna da kayan aikin  ga cibiyoyin kiwon lafiya a gundumomi 10.

An gudanar da bikin mika kayan a Cibiyar Musulunci ta Gwarzo, inda Shugaban Karamar Hukumar Dakta Mani Tsoho Abdullahi, wanda ya sami wakilcin mataimakinsa Alhaji Abdulmumin Garba Lakwaya, ya jagoranci taron.

Kayayyakin da aka raba sun haɗa da na’urar auna hawan jini, na gwajin siga, da wasu kayan aiki daban-daban da aka tanada domin ƙarfafa aikin cibiyoyin lafiya tare da faɗaɗa damar jama’a na samun ingantacciyar kulawa.

Yayin da yake jawabi, Lakwaya ya jaddada bukatar ma’aikata su jajirce wajen aiki da gaskiya da rikon amana. Ya tunatar da su cewa an samar da  kayayyakin ne domin amfanin marasa lafiya kai tsaye,  daidai da kudirin  karamar hukumar wajen samar da ingantaccien kiwon lafiya.

Mataimakin Shugaban ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da kuma Dakta Gwarzo bisa ci gaba da ƙoƙarin inganta rayuwar jama’a.

Shi ma Kansilan Lafiya na Karamar Hukumar, Alhaji Nazifi Gambo Salihawa, ya jawo hankalin cibiyoyin lafiya kan bin ƙa’idojin rahoton lafiya na Najeriya, inda ya bukace su da su tabbatar da bin ka’ida wajen rubuta da kuma amfani da sabbin kayayyakin domin samun inganci, da kuma amincewar al’umma.

Wasu daga cikin shugabannin cibiyoyin da suka karɓi kayayyakin sun tabbatar da cewa za a raba magungunan bisa adalci tare da amfani da su yadda ya dace domin biyan bukatun lafiya na jama’a.

Taron ya samu halartar Kakakin Majalisar Karamar Hukumar, kansiloli, shugabannin cibiyoyin lafiya, da sauran masu ruwa da tsaki.

 

Daga Khadijah Aliyu

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara