Labarai
Majalisa Wakilai Ta Yabi Jihar Jigawa Kan Dorewar Shirye-shiryen Lafiya Ga Kowa
Kwamitin kula da harkokin lafiya na majalisar wakilai ya yaba wa jihar Jigawa bisa kasancewarta jagaba a shirin samar da lafiya ga kowa ta hanyar manyan sauye-sauye da kuma kudaden da ake kashewa wajen kara inganta fannin.
Yabon ya fito ne lokacin da kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Honorable Amos Gwamna Magaji, ya kai ziyarar ban girma ga Gwamna Umar Namadi a gidan gwamnati Dutse.
Hon. Magaji ya bayyana gamsuwa da irin nasarorin da jihar ta cimma musamman wajen ware sama da kashi 15 cikin 100 na kasafin kuɗin shekara-shekara ga harkokin lafiya.

Ɗan majalisar ya kuma taya gwamnan murna bisa nasarar lashe kyautar dala 500,000 na Primary Health Care Leadership Challenge Award, yana mai cewa hakan shaida ce ta irin cigaban da jihar ke samu a tsarin gyaran fannin lafiya.
Hon. Magaji ya kara yaba da matakin gwamnatin jihar na daidaita albashin ma’aikatan lafiya da na tarayya, yana mai cewa wannan zai rage barin ƙwararru su fita ƙasashen waje, wanda hakan zai iya jawo wasu daga sauran jihohi zuwa Jigawa.
A nasa jawabin, Gwamna Namadi ya gode wa ‘yan majalisar bisa yabon da suka yi, tare da jaddada kudirin gwamnatinsa na mayar da fannin lafiya ginshikin cigaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma.

Gwamnan ya jaddada cewa ilimi, da cigaban tattalin arziki, da samar da aiki na iya bunkasa ne kawai idan jama’a suna cikin koshin lafiya.
Ya bayyana cewa gwamnatin sa ta fi mayar da hankali wajen karfafa cibiyoyin lafiya na farko a matsayin ginshikin samar da ayyukan lafiya, tare da shirin kafa wani cibiyar lafiya da za ta ƙunshi cibiyar bincike, cibiyar cututtukan zuciya, da masana’antar iskar taimakawa numfafashi wato oxygen.
Gwamna Namadi ya tabbatar wa kwamitin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauye tare da yin aiki kafada-da-kafada da majalisar tarayya domin cimma burin samar da lafiya ga kowa a jihar Jigawa.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai5 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai6 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai6 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai6 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
-
Labarai3 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
