Ilimi
Shugabar Kwalejin Fasahar Sadarwa Da Adana Bayanai Ta Jigawa Ta Kai Ziyara Ga Sarkin Kazaure
Mai martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Najib Husaini Adamu, ya bada tabbacin hadin kai da goyon bayan sa ga sabuwar shugabar Kwalejin fasahar sadarwa da adana bayanai ta jihar Jigawa dake Kazaure, Farfesa Habiba Adamu Kakudi domin karfafa cigaban Kwalejin.
Mai martaba Sarkin Kazaure ya bada wannan tabbaci ne lokacin da tawagar sabuwar shugabar Kwalejin ta ziyarci shi a fadar sa.

Alhaji Najib Husaini Adamu ya bayyana nadin mace domin ta shugabanci wannan kwaleji a matsayin wani muhimmin mataki a ci gaban rayuwar al’umma.
Mai Martaban ya yi kira ga mahukuntan kwalejin da sauran masu ruwa da tsaki da su ba ta hadin kai da goyon baya domin gudanar da ayyukan ta ba tare da wani nakasu ko bambamci ba.
Tun da farko, shugaban riko na kwalejin Dr. Said Adamu yace sabuwar shugabar ba bakuwa ba ce kasancewar ta yi aiki a matsayin wakiliya a hukumar gudanarwar kwalejin daga bisani ta zamo shugabar hukumar gudanarwa kawo wannan mataki da aka nada ta a yanzu.

A na ta jawabin, sabuwar shugabar Kwalejin fasahar sadarwa da adana bayanai ta jihar Jigawa da ke garin Kazaure, Farfesa Habiba Adamu Kakudi tace tawagar ta ziyarci fadar Mai martaba sarki ne don neman tabarraki da goyon bayansa domin samun nasarar gudanar da ayyukan ta.
Kazalika, ta bada tabbacin aiki tare da sauran masarautun jihar domin kara kawo abubuwan da za su ciyar da Kwalejin gaba.
A nata jawabin, uwar gidan shugaban majalisar dokokin jihar Jigawa, Hajiya Zaharau Haruna Aliyu Dangyatin ta godewa Mai martaba sarki bisa kudurin sa na goyon baya ga sabuwar shugabar Kwalejin.

Ta kuma bada tabbacin cewar sabuwar shugabar za ta yi dukkan mai yiwuwa domin sauke nauyin dake kan ta na ciyar da wannan kwaleji gaba a fagen fasahar sadarwa da adana bayanai.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
