Labarai
Kashim Shettima Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Shugaba Tinubu Gabanin Zaben 2027
Daga Bello Wakili
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cikakken kwarin gwiwa ga jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Ya bayyana hakan ne a taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar APC da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Abuja.
Shettima ya bayyana cewa duk wanda ke ƙalubalantar Shugaban Ƙasa, zaɓi ne na siyasa da mutum ya ɗaukar ma kansa, wanda a karshe zai kai shi ga cizon yatsa.
Ya jaddada cewa duk da cewa Najeriya ƙasa ce ta dimokiraɗiyya inda kowa ke da ’yancin tsayawa takara, tarihin ayyuka da gogewar Tinubu sun sanya shi kaiwa ga wani babban matsayi da ya kamata a jinjina masa.
Shettima ya kuma lura da cewa nasarar zaɓe ta wuce shahara a yanar gizo kawai, yana mai jaddada cewa ba a cin zaɓe ta hanyar hulɗa da kafafen sada zumunta ko hayaniyar jama’a kaɗai.
Ya nuna muhimmancin haɗin kan jama’a, bin gaskiya da sadaukarwa, yana mai cewa irin waɗannan abubuwa ne ke tabbatar da nasara a rumfunan zaɓe, ba fafutuka ko shashi fadi a yanar gizo ba,
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
