Labarai
Jam’iyyatut Takaful Aytam Ta Ziyarci Marasa Lafiya A Asibiti Dake Kaduna
Kungiyar Jam’iyyatut Takaful Aytam dake Kaduna ta ba da gudunmuwar kuɗi ga marasa lafiya dake kwance a asibitin Yusuf Dantsoho dake Kaduna.
Shugabar kungiyar, Malama Rabi’atu Adam Isma’il wadda ta jagoranci wakilan kungiyar zuwa asibitin, tace, wannan wani bangare ne na ayyukanta, su taimakawa mabukata a lokacin wannan wata mai albarka na Ramadan.

Malama Rabi’atu Adam Isma’il ta yi bayanin cewa, yana daga cikin koyarwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW a ziyarci mara lafiya da ciyarda marayu da marasa karfi a lokacin azumin watan Ramadan da sauran lokuta.
Ta yi nuni da cewa, ba gwamnati ko wasu kungiyoyin kasashen waje ke tallafawa kungiyar ba, suna samun kudadensu ne ta hanyar tara taro-sisi a tsakanin wakilan kungiyar da wasu daidaikun jama’a.
Malama Rabi’atu Adam Isma’il ta ce, kungiyar, ta baiwa kusan kowane majinyaci naira dubu wanda babu yawa, sai dai zai taimaka ma marasa lafiyan wajen sayen magani ko kayan marmari.
Ta nemi ganin gwamnati da mawadata da kungiyoyi masu zaman kansu su tallafawa kungiyar domin ta yi abinda ya fi haka a gaba wajen yi wa al’uma hidima.
A nata tsokacin, mataimakiyar shugabar kungiyar, Malama Ruqayya Ahmad Bashir ta ce, wakilai da abokanan kungiyar ne suka yanke shawarar harhada dan abinda Allah Ya hore musu domin tallafawa marasa lafiyan dake kwance a asibiti.
Ta kara da cewa, sun baiwa marasa lafiyan gudunmuwar ne ta hanyar nuna soyayya da tausayi, ta yi musu addu’ar samun lafiya cikin gaggawa.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana, Saleh Muhammad da Fatima Umar sun yabawa jagororin kungiyar akan tallafin kudin, sun yi addu’ar Allah Ya sa ka musu da mafificin sakamako.
Kungiyar ta ziyarci babban dakin marasa lafiya da dakin masu karaya ko quna da kuma dakin masu hatsari.
Khadija Kubau
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik

