Connect with us

Labarai

Harin Ta’addanci: Gwamnatin Katsina Bukacin Hadin Kan Al’ummar Jihar

Published

on

Gwamnatin Jihar Katsina ta yi kira ga al’ummomin da ke zaune a yankunan da ake fama da matsalolin tsaro da su ba da haɗin kai ga jami’an tsaro a ci gaba da yaƙi da ‘yan ta’addanci da masu garkuwa da mutane.

Mukaddashin Gwamnan Jihar, Alhaji Faruk Jobe ne ya yi wannan kira bayan taron gaggawa maga da al’amuran tsaro da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Katsina.

Jobe ya bayyana cewa an kira taron ne domin sake tantance tsarin tsaron jihar da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa mai tasiri tsakanin hukumomin tsaro wajen yaƙi da ta’addanci, da yin sintiri a yankuna da kuma musayar bayanai domin tabbatar da nasarar yaƙi da ‘yan bindiga.

Ya ce bisa ga rahotannin baya-bayan nan daga shugabannin hukumomin tsaro daban-daban, jami’an tsaro na iya bakin ƙoƙarinsu, amma ba za a iya samun gagarumar nasara ba, ba tare da tallafi da haɗin kai daga al’ummomi ba.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa a fannin kayan aikin soja, Jihar Katsina ce tafi shirye-shirye a shiyyar Arewa maso Yamma, tana da motoci masu sulke 43, kayan sintiri da na yaƙi, tare da  jajirtattun jami’an Sojojin Najeriya, Rundunar Sama, ‘Yan sanda, DSS, ‘yan sa-kai, mafarauta da kuma jami’an tsoro na jihar wato Community Watch Corps.

Yayin da yake bayyana harin da aka kai a Unguwar Mantau da ke Karamar Hukumar Malumfashi a matsayin aikin ta’addanci na rashin imani, Jobe ya yi ta’aziyya ga mutanen yankin tare da tabbatar da cewa za a kamo masu laifin kuma a hukunta su bisa doka.

Ba za mu huta ba sai mun kawar da ta’addancin ‘yan bindiga daga jihar nan, sai dai muna bukatar haɗin kai sosai daga al’umma musamman a fannin bayar da bayanai. Dakarunmu ba za su iya aiki su kaɗai ba, suna buƙatar haɗin kai daga al’ummomi.”

 

Daga Isma’il Adamu

 

 

Labarai

Labarai4 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai1 day ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai1 day ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai1 day ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara