Labarai
NEMA Da Masu Ruwa Da Tsaki Sun Kara Haɗa Gwiwa Don Hana Aukuwar Ambaliya Da Hadarin Tankar Mai
By Adamu Yusuf
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), tare da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki da ke kula da harkokin bala’o’i a Jihar Kaduna, sun sake haɗa karfi da karfe domin rage aukuwar bala’o’i a wannan shekarar.
Da yake magana a wajen taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a ofishin NEMA da ke Kaduna domin duba abubuwan da suka faru na bala’o’i a shekarar da ta gabata, Shugaban Ayyuka na hukumar NEMA mai kula da jihohin Katsina da Kaduna, Suleiman Mohammed, ya ce hukumar ta sauya tsarin aikin ta daga bayar da taimako gaggawa bayan bala’i ya faru zuwa ɗaukar matakan kare faruwar bala’i baki daya.

Ya bayyana cewa bayan hukumomin da suka dace kamar Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya sun fitar da hasashen yanayi na kakar daminan bana, hukumar NEMA ta shirya irin wannan taron masu ruwa da tsaki tun farkon shekarar domin nazarin yiwuwar illolin da ka iya tasowa tare da tsara hanyoyin da za a bi wajen shawo kan bala’o’i.
A cewarsa, taron ya haɗa manyan masu ruwa da tsaki da suka tattauna hanyoyin da za su yi aiki tare wajen tunkarar bala’o’i tun kafin su faru da lokacin da suke faruwa, da kuma bayan sun faru.
Suleiman Mohammed ya kuma bayyana cewa haɗin gwiwar hukumomi kamar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA), Kungiyar Red Cross, Hukumar Kashe Gobara, Civil Defence da sauran hukumomi ya taimaka wajen magance wasu bala’o’i da suka faru a jihar a shekarar da ta gabata, ciki har da ambaliya, gobara da kuma hatsarin tankokin mai.
Ya tuna cewa an gudanar da wani atisayen kwaikwayo kan yadda za a magance hatsarin tankokin mai a Maraban Jos, domin nuna yanda hukumar take gudanar da ayyukan ceto da agajin gaggawa.
Ya ce, “Atisayen wanda ya haɗa da direbobin tankokin mai da sauran masu ruwa da tsaki, an shirya shi ne domin ƙarfafa shirin ko-ta-kwana da kuma tabbatar da haɗin gwiwar da ya dace idan irin waɗannan bala’o’i suka faru.”
Ya ƙara da cewa duk da cewa an samu wasu ambaliyar ruwa a yankuna kamar Kaduna North, Kaduna South, Zaria da kuma ƙaramar hukumar Sanga, saurin ɗaukar mataki da hukumomin agaji suka yi ya taimaka wajen rage illolin da bala’in ya jawo ga al’ummomin da abin ya shafa.
Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban Sashen Kula da Bala’o’i na Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (NSCDC) a Jihar Kaduna, Mataimakin Kwamandan Hukumar Akaine King Michael, ya bayyana taron a matsayin mai muhimmanci kuma da ya zo a kan lokaci domin nazarin ayyukan kula da bala’o’i na shekarar da ta gabata.
Ya ce taron ya ba masu ruwa da tsaki damar tantance abubuwan da suka faru a shekarar 2025, musamman hatsarin tankokin mai da ke ɗauke da man fetur, wanda sau da dama kan haddasa zubar mai a kan hanyoyi tare da jefa rayuka da dukiyoyi cikin haɗari.

Michael ya kuma bayyana cewa hukumar NSCDC na ci gaba da aiki tare da NEMA wajen gudanar da ayyukan ceto yayin bala’o’i, inda ya ce babban aikin su shi ne fitar da mutanen da abin ya shafa daga wuraren haɗari, kulle wuraren da lamarin ya faru da kuma hana jama’a ɗiban mai idan tankar mai ta yi hatsari..
A nata jawabin, Shugabar Sashen Muhalli da Sauyin Yanayi da Makamashi na Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) a Jihar Kaduna, Rahmatu Suleiman, ta bayyana muhimmiyar rawar da hukumar ke takawa wajen wayar da kan jama’a da kuma haɗa kai da al’umma domin hana aukuwar bala’o’i.
Ta ce NOA na aiki kafada da kafada da NEMA wajen isar da saƙonnin wayar da kai ga al’ummomi a faɗin jihar, inda ta bayyana cewa hukumar na da ma’aikata a dukkan ƙananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna da ke gudanar da wayar da kan jama’a kan haɗarin bala’o’i kamar ambaliya.

Rahmatu Suleiman ta ƙara da cewa hukumar na kuma aiki tare da kafafen yaɗa labarai domin ƙara wayar da kan jama’a, inda ta bayyana cewa Daraktan NOA na Jihar Kaduna, Danjuma Makama, kan bayyana a kafafen yaɗa labarai sau da dama domin ilmantar da jama’a kan matakan kariya da kuma hanyoyin rage illolin ambaliya da sauran bala’o’i.
Mahalartar taron sun jaddada muhimmancin ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, shugabannin al’umma da kuma jama’a domin hana aukuwar bala’o’i da kuma tabbatar da saurin kai dauki idan suka faru.
Sun kuma yi kira a ci gaba da gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a domin gujewa halayen da kan jawo hatsari ko ƙara tsananta matsaloli, musamman a lokutan hatsarin tankokin mai da kuma ambaliya.
-
Labarai6 days agoAna Zargin Mutum 140 Sun Bace Bayan Nutsewar Jirgin Ruwan Iran a Gaɓar Sri Lanka
-
Labarai7 days agoJam’iyyar APC Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni a Jihar Kano
-
Labarai5 days agoRamadan: Sarkin Kauru Ya Bukaci a Kara Karfafa Tsaro Tare da Tallafawa Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Miliyoyin Naira Don Sayen Gidaje 96 Daga Gwamnatin Tarayya
-
Labarai4 days agoKaramar Hukumar Birnin Kudu ta Nemi Hadin Kan Kungiyar ‘Yan Achaba Wajen Dakile Matsalar Tsaro
-
Labarai4 days agoSojojin Najeriya Sun Karɓi Motocin Yakin Da Aka Kera A Cikin Ƙasa
-
Ilimi6 days agoGwamnatin Tarayya da ke Gusau za ta Kafa Cibiyar Nazari kan Tarihi da Al’adun Zamfara
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kano Ta Fara Shari’ar Tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam
