Labarai
An Cire Rai Daga Ceto Wadanda Suka Makale A Karkashin Gine-gine Samakon Ambaliyar Ruwa A Pakistan
Masu aikin ceto a Pakistan sun sanar da cire rai daga yiwuwar iya ceto masu sauran lumfashi a ƙarƙashin gine-ginen da suka rushe a zaftarewar lakar da ƙasar ta gani sakamakon mamakon ruwan sama da ya haddasa ambaliya, wanda kawo yanzu ya kashe mutanen da yawansu ya kai 344.
Bayan tono mai zurfi a tarin laka da baraguzan gine-ginen da suka rushe, masu aikin ceton a yammcin jiya Lahadi sun ce babu tabbacin iya samun masu sauran numfashi a ƙarkashin laka, a wani yanayi da har yanzu ake neman mutanen da yawansu ya haura 150 da suka yi ɓatan dabo tun bayan ibtila’in na ƙarshen makon jiya.
Tun daga Alhamis ɗin makon jiya Pakistan ke ganin mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wani ɓangare na ƙaƙƙarfan ruwan da bisa al’ada ƙasashen kudancin Asia ke gani duk shekara, tun daga ƙarshen watan Yuni zuwa farkon watan Satumba ko ƙarshen Yuni, da akan ga zubar ruwa mai yawan gaske haɗe da iska mai ƙarfi da kuma tsawa, wanda a lokuta da dama ke haddasa asarar ɗimbin rayuka.
Tuni ambaliyar ta haddasa rushewar ɗaruruwan gidaje yayin da ƙauyuka da dama ruwa ya cikasu kuma suka rasa hanyar fita daga inda suke, kodayake lamarin ya fi tsananta a yankin Khyber na Lardin Pakhtunkhwan inda mutane 317 suka mutu.
Bayanai sun ce gidaje da dama sun zama kango bayan da ambaliyar ta kashe dukkanin iyalan a gefe guda kuma masana ke gargaɗin cewa a nan gaba ne za a ga zubar ruwan mafi yawa wanda galibi ke cika tekuna da kan kai ga tumbatsarsu.
A yankin Buner mutane 150 suka ɓace yayin da wasu 208 suka mutu, sannan aka shafe kauyuka 10 zuwa 12.
Kamfanin dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa jami’an agaji aƙalla dubu biyu ke aikin ceto.
rfi
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
