Connect with us

Ilimi

Hukumar Ilimantar Da Makiyaya Ta Kasa Ta Horarda Ma’aikatanta Kan Yanda Za’a Mayarda ‘Ya’yan Makiyaya Makaranta 

Published

on

 

By Adamu Yusuf

 

Hukumar Ilimantar da Makiyaya Ta Kasa (NCNE) ta shirya taron horas da ma’aikatan ta kan tsaftace bayanai da rubuta rahotanni da zai taimaka wajen rage karuwar yawan yara da basu zuwa makaranta a cikin al’ummomin makiyaya a kasar nan.

 

Babban Daraktan a Hukumar, Dr. Abdu Umar Hardo, ya bayyana hakan yayin bude taron da aka gudanar a hedkwatar hukumar dake Kaduna.

 

Dr. Umar Hardo ya ce horon yana karkashin hadin gwiwa ne tsakanin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da Hukumar Ilimantar da Makiyaya ta kasa da Hukumar Ilimin da Al-Majirai da Hukumar Ilimintar da Jama’a (NCME) da dai sauransu.

Ya kara da cewa shirin yana nufin baiwa ma’aikata kwarewa wajen nazari da sarrafa bayanan da aka tattara da aka samo domin aiwatar da shirye-shiryen don rage yawan yaran makiyaya da basa zuwa makaranta.

 

Dr. Hardo ya ce hukumar an dora mata alhakin rage yawan yara da basu zuwa makaranta ba a cikin al’ummomin makiyaya kawai ba har da masu kamun kifi da manoma a fadin kasar.

 

A cewarsa, kimanin yara miliyan 5.5 daga al’ummomin makiyaya ba sa zuwa makaranta a yayin da kimanin yara miliyan 1.5 ke halartar makaranta, lamarin da ke nuna babban gibi da shirin ke nufin magancewa.

 

Ya kara da cewa kwanan nan hukumar ta gudanar da binciken taswira a jihohi shida da Babban Birnin Tarayya (FCT), ciki har da Jigawa, Gombe, Nasarawa, Enugu, Cross River, da Oyo, inda aka gano kimanin yara da matasa 660,000 da basu zuwa makaranta ba.

 

A jawabin sa, Professor Aminu Abdul Bichi, kwararre daga African Institute for Solution Development, ya ce horon ya mayar da hankali ne kan kididigar bayanai da aka samu wanda hakan zai taimaka wajen tsara yanda za’a dawo dasu makaranta.

 

Professor Bichi ya bayyana cewa nazarin bayanai ya nuna cewa kimanin kashi 62 cikin 100 na yara makiyaya ba su zuwa makaranta, yayin da kashi 32 cikin 100 suka daina zuwa makaranta a matakin firamare.

 

Ya kara da cewa 3.2 cikin 100 sun daina makaranta a matakin sakandare na farko, yayin da 1.2 cikin 100 suka daina a sakandare na gaba.

 

Professor Bichi ya ce wadannan bayanai sun nuna babbar matsalar kuma suna nuni da bukatar shirye-shirye na musamman da suka dogara da bayanai domin tabbatar da cewa yara daga al’ummomin makiyaya suna samun damar ilimi.

 

A ganawa da Radio Nigeria, Daraktar Tsare-Tsare, Bincike da Kididdiga a Hukumar, Dr. Rose Nkechi Nwaji, ta ce rungumar Shirin Ilimin Firamare Na musamman zai taimaka wajen rage yawan yara da basu zuwa makaranta musamman a cikin al’ummomin makiyaya.

 

Dr. Nwaji ta ce shirin, zai baiwa yara da suka daina zuwa makarantar damar karatu domin su shiga tsarin ilimi na kasa.

Ana sa ran mahalarta horon za su nazarci bayanan da aka tattara domin amfanin da su wajen tsara manufofi da za’a yi amfani dasu wajen maganin matsalar rashin zuwa makaranta na yaran makiyaya ta amfanin da sabon Shirin Ilimin Firamare na (ABEP).

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara