Kasuwanci
Jihar Kwara Ta Samar Da Rijiyar Burtsatse Mai Amfani Da Hasken Rana Ga Makiyaya
Shirin Taimakawa da Ƙarfafa Samar da Amfanin Dabbobi na Jihar Kwara (L-PRES) ya mika sabon aikin rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana ga al’ummar Fulani da ke ƙaramar hukumar Asa a Jihar Kwara.
Yayin bikin mika aikin, jami’in kula da shirin na L-PRES a Jihar, Mista Olusoji Oyawoye, ya bayyana cewa aikin yana cikin kokarin gwamnatin jihar na rage rikici tsakanin manoma da makiyaya.
Wacce ta wakilce shi, jami’ar kula da walwalar jama’a ta shirin, Hajiya Folake Iseyemi, ta ce wannan yunƙuri zai taimaka wajen ƙarfafa juriyar makiyaya dangane da sauyin yanayi da ake fuskanta, da kuma ƙara yawan dabbobin da ake sanarwa.
Ya bayyana cewa aikin ya yi daidai da babban burin ci gaba na shirin L-PRES, yana mai cewa an kafa wani kwamiti mai mutum biyar daga cikin al’umma da ke da alhakin tabbatar da dorewar aikin a matakin ƙauyuka.

Oyawoye ya ƙara da cewa kwamitin tare da ofishin da ke da alhakin jagorantar shirin zai gudanar da ayyukan da za su ƙarfafa dangantaka tsakanin manoma da makiyaya, hana rikice-rikice, da kuma samar zaman lafiya tsakanin al’ummomi daban-daban a yankin.
A jawabinsa a madadin al’ummar Fulani, Jowuron Labintan, Alhaji Ibrahim Hamadu, ya gode wa gwamnatin Jihar Kwara, Shirin L-PRES da sauran abokan hulɗa bisa wannan karamcin.
Ya bayyana cewa aikin zai rage musu yawan ƙaura wajen neman ruwa, tare da dakile matsalolin rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin da kuma cikin jihar baki ɗaya.
Alhaji Hamadu ya kuma roƙi ƙarin ayyukan da za su rage wahalhalun da makiyaya ke fuskanta, domin bunkasa kiwo da kuma ƙara wadatar abinci a ƙasar.
A yayin bikin, an raba ababen da za su taimakawa makiyayan wajen kiwo, da suka hada da gishirin dabbobi da sauransu.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
