Connect with us

Labarai

Iyalan Muhammadu Buhari Sun Bayyana Godiyarsu Ga ‘Yan Najeriya Da Sauran Kasashen Duniya

Published

on

Iyalan tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari sun bayyana godiya ta musamman ga ‘yan Najeriya da al’ummomin kasashen duniya bisa goyon baya da nuna alhini lokacin rasuwar marigayin.

A cikin wata sanarwa da Malam Garba Shehu ya sanyawa hannu a madadin iyalan, ta bakin Malam Mamman Daura, sun mika godiya ta musamman ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mai dakinsa, Sanata Remi Tinubu, bisa kulawar da suka nuna kafin, da kuma bayan rasuwar tsohon shugaban kasar.

Irin ziyarce-ziyarcen da aka kai, saƙonnin jaje, da kuma yanke hukuncin ayyana hutu da kuma canza sunan Jami’ar Maiduguri zuwa Buhari, duk sun kasance alamu ne na tausayawa da suka sanya mana kwarin gwiwa ” in ji iyalan.

Hakazalika sun jinjinawa  mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, wanda ya yi tafiya zuwa Birtaniya sannan ya kai ziyara Daura tare da wasu ministoci a lokacin makokin. “Hakan ya karfafa mana gwiwa wajen fuskantar wannan babban rashi,” in ji sanarwar.

Iyalan sun kuma gode wa manyan shugabannin duniya, ciki har da Sarki Charles III na Birtaniya, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, da mataimakiyar  Amina Mohammed, Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka (AU), da shugabannin kasashen ECOWAS bisa jajentawa, wasiku, da ziyarar gaisuwa ko kiran waya.

Sun kuma yaba da ziyarce-ziyarce da sakonni daga shugabannin Najeriya na yanzu da na baya, ciki har da tsofaffin shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar, tsofaffin mataimakan shugaban kasa Atiku Abubakar, Namadi Sambo, Yemi Osinbajo, da Ambasada Babagana Kingibe.

Gwamnonin jihohi daban-daban musamman gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umar Radda, gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, da tsohon gwamnan jihar Anambra Dr. Peter Obi, duk sun samu yabo bisa irin tausayin da suka nuna.

Sanarwar ta kara da godiya ga shugabannin Majalisar Tarayya ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin, da sauran ‘yan majalisa na matakin kasa da jihohi.

“Har ila yau muna jinjina ga Sarakuna daga sassa daban-daban na Najeriya, ciki har da Nai Alfarma Sarkin Musulmai, Shehun Borno, da sarakunan Gwandu, Katsina, da Daura.”

Iyalan Buhari sun kuma gode wa shugabannin addinai da na al’umma, kungiyoyin matasa, mata, ‘yan siyasa, ma’aikata, jami’an tsaro, da kafafen watsa labarai da suka shiga cikin al’amuran makokin.

Sai kuma manyan ‘yan kasuwa da suka hada da Aliko Dangote, Abdul Samad Rabiu, Muhammadu Indimi, Dahiru Mangal, Kola Adesina, wadanda su ma sun kasance da iyalan marigayin yayin jimamin rashinsa.

Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya jagoranci Najeriya daga shekarar 2015 zuwa 2023, ya rasu a Birtaniya a farkon wannan wata. An binne shi a mahaifarsa ta Daura a jihar Katsina.

 

Bello Wakili

Labarai

Labarai6 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai8 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara