Labarai
Shugaba Tinubu Ya Bayyana Kaduwarsa Bisa Rasuwar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa bisa rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka fitar daga fadar shugaban kasa, wacce ta ce tsohon shugaban Ƙasa ya rasu a yau Lahadi da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a birnin London, bayan fama da doguwar jinya.
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya yi magana da uwargidan marigayin, Hajiya Aishatu Buhari, inda ya mika ta’aziyyarsa ta musamman gare ta.
Shugaba Tinubu ya kuma umurci Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da ya tafi ƙasar Birtaniya domin rakiyar gawar tsohon Shugaban Ƙasa Buhari zuwa gida Najeriya.
An zabi Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban Ƙasa sau biyu – a shekarar 2015 da kuma 2023.
Haka kuma, ya shugabanci ƙasar a matsayin Shugaban Mulkin Soja daga watan Janairu 1984 zuwa watan Agusta 1985.
Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a sassauta tuta a faɗin ƙasa, a matsayin alamar girmamawa ga mamacin.
Daga Bello Wakili
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
