Labarai
Gwamna Namadi Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Muhammadu Buhari
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana alhininsa bisa rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar ga manema labarai a Dutse, Gwamna Namadi ya bayyana marigayi Muhammadu Buhari a matsayin jagora mai daraja wanda ya yi wa Najeriya hidima tare da sadaukar da kai.
Malam Umar Namadi ya mika sakon ta’aziyya a madadin gwamnatin da al’ummar Jihar Jigawa ga iyalan marigayi shugaban kasa, yana addu’ar Allah ya ba su hakuri da juriyar wannan babban rashi.
Haka kuma, ya mika ta’aziyyarsa ga Shugaban Ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, gwamnatin da al’ummar Jihar Katsina, da al’ummar Najeriya baki daya.
A cewarsa, marigayi Shugaba Buhari zai ci gaba da kasancewa a zukatan ‘yan Najeriya saboda jajircewarsa ga hadin kan ƙasa da ci gabanta, da kuma shugabancinsa na gaskiya da sadaukarwa ga aikin gwamnati yayin rasuwarsa.
Namadi ya ƙara da cewa, Jihar Jigawa tana cikin jimamin wannan babban mutum tare da yin addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya sa Aljannah makomarsa.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
