Ilimi
Shugaban Majalisar Nasarawa Ya Yi Alhinin Rashin Tsohon Minista Da Ya Rasu Yana Da Shekaru 70
Kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa Dr. Danladi Jatau ya bayyana matukar kaduwarsa dangane da labarin rasuwar tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja, Barista Solomon Aku Ewuga.
Kakakin majalisar a wata sanarwa da sakataren yada labaran sa Jibrin Gwamna ya fitar, ya bayyana rasuwar mataimakin gwamnan jihar a matsayin babban rashi ga jihar da ma Najeriya baki daya.
Sanarwar ta ruwaito shugaban majalisar na cewa rasuwar tsohon sanata mai wakiltar nasarawa ta arewa, mutuwa ce da ta girgiza al’ummar jihar Egu da ma jihar baki daya ba.
“Bishiyar Iroko ta fado, mai taimakon jama’a kuma fitaccen dan siyasa ya je gida ya huta, Allah ya kara masa yarda.” Inji Shugaban Majalisar.
Kakakin Majalisar Danladi Jatau ya bayyana Sanata Solomon Ewuga a matsayin maginin gada wanda ya taba rayuwar jama’a da dama, ya kuma jajirce wajen samar da zaman lafiya da hadin kai da cigaba a tsakanin al’umma sannan kuma ya bayar da tasiri da gudummawa sosai a fagen siyasa da sauran al’amuran bil’adama.
Dokta Danladi Jatau wanda ya yaba da kyawawan halayen Solomon Ewuga ya roki Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma saka masa da ayyukansa na alheri da ya aiwatar.
Rel/Aliyu Muraki/Lafia.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
