Labarai
Isra’ila Ta Kashe Kananan Yara Masu Dibar Ruwa A Gaza
Hukumar bayar da agajin gaggawa a Gaza ta ce aƙalla mutum 10, ciki har da ƙananan yara guda shida ne suka rasu a sanadiyar harin da Isra’ila ta kai ta sama a Gaza a safiyar Lahadi.
An kai gawarwakin waɗanda suka rasu zuwa asibitin Nuseirat’s al-Awda, inda wani likita ya ƙara da cewa sun yi jinyar wasu mutum 16, ciki har da ƙananan yara guda bakwai.
Wani ganau ya ce jirgi mara matuƙi ne ya harba makami mai linzami a kan dandazon mutanen da suka yi layi riƙe da jarkunansu domin ɗibar ruwa daga wata tankar ruwa a sansanin ƴangudun hijira na al-Nuseirat.
Har zuwa haɗa wannan rahoton, rundunar tsaron Isra’ila ba ta ce komai ba kan batun.
Wani faifan bidiyo da BBC ba ta tantance ba ya nuna ƙananan yara jina-jina, da gawarwakin wasu, wasu kuma suna ta ihu, sannan wasu suka zo daga bisani suna kwashe mutanen zuwa asibiti a motoci da amalanke.
Isra’ila ta fara kai hare-hare ne a Gaza tun bayan harin Hamas a ƙasar a ranar 7 ga Oktoban 2023, inda ƴan Hamas ɗin suka kashe 1,200, sannan suka yi garkuwa da wasu 251.
Zuwa yanzu Isra’ila ta kashe aƙalla mutum 57,882 a Gaza, kamar yadda ma’aikatar lafiyar yanki ta bayyana.
Haka kuma an tarwatsa sama da kashi 90 na gidajen zirin, sannan an lalata asibitoci da cibiyoyin ruwan sha da sauran abubuwan more rayuwa, wanda hakan ye jefa yankin cikin ƙarancin abinci da magani da man fetur.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
