Labarai
Malaman Jami’o’in Isra’ila Sun Nemi Jamus Ta Tilasta Dakatar Da Yakin Gaza
Malaman jami’o’i sama da 100 daga Isra’ila sun bayyana cewar jan kafar da ƙasar Jamus ke yi wajen ɗaukar matakin matsin lamba ga gwamnatin Isra’ila na iya bai wa ƙasar damar ci gaba da aikata manyan laifuffuka a Gaza.
Wata wasika da masanan suka rubuta wa ɗaya daga cikin manyan shugabannin jam’iyyar SPD da ke mulki a Jamus, ta ce rashin ɗaukar matakin na iya bada damar gudanar da wasu sabbin laifuffuka a Gaza, tare da watsi da irin tarihin da aka koya a shekarun baya.
A ranar 22 ga watan Yuli, biyu daga cikin jiga jigan kawancen jam’iyyun dake jagorancin Jamus, sun bukaci ƙasar da ta shiga cikin ƙasashen duniya da ke ƙawance domin gaggauta kawo ƙarshen yaƙin Gaza da kuma sanya takunkumi a kan Isra’ila da kuma kin sayar mata da makamai.
Gwamnatin Jamus da ke ƙarƙashin ƙawance jam’iyyun CDU da SCU da kuma SPD ta ƙarfafa sukar da take yiwa gwamnatin Isra’ila a kan yadda take azabtar da mazauna Gaza wajen hana kai musu kayan agaji, amma kuma ya zuwa yanzu bata bayyana ɗaukar wasu matakai masu tsauri ba.
Isra’ilar dai ta yi watsi da duk wani yunkuri na zargin da ake mata na amfani da yunwa wajen azabtar da mutane akalla miliyan biyu dake zama a Gaza, inda ta bayyana cewar ƙungiyar Hamas ce ke sace abincin da ake kai wa mutanen yankin.
Matakan kai hari a kan masu neman kayan agajin da Isra’ila ke yi a kan mazauna Gazar, sun yi sanadiyar hallaka akalla mutane sama da dubu guda.
Kungiyar Hamas ta ƙaddamar da harin da ya hallaka Yahudawa sama da 1,200 a watan Oktobar shekarar 2023, abinda ya sa Isra’ila ƙaddamar da yakin da ya hallaka mutane sama da 50,000 a bangaren Falasdinawa.
Tuni ƙasashen Birtaniya da Canada da kuma Faransa suka bayyana aniyarsu ta amincewa da ƙasar Falasdinu a taron Majalisar Ɗinkin Duniyar da zai gudana a watan Satumba, inda suke cewa ta wannan hanyar ce kawai za a samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Isra’ila da Amurka sun bayyana matuƙar ɓacin ransu da matakin, yayin da a yau Firaminista Benjamin Netanyahu ke cewa ba zai dakatar da yakin da yake yi ba har sai ya murkushe ƙungiyar Hamas.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
