Ilimi
Gwamnatin Kano Za Ta Farfado Da Makarantu Tare Da Kara Inganta Fannin Ilimi
Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudurinta na farfado da harkar ilimi ta hanyar gyara makarantun da suka lalace wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata.
Da yake jawabi yayin wata ziyarar duba makarantu a Makarantar Sakandare ta Murtala Muhammad da ke ƙaramar hukumar Tarauni, Kwamishinan Ilimi, Dr. Ali Haruna Makoda, ya bayyana halin da wasu makarantu ke ciki a matsayin alamar rushewar tsarin ilimi.
Kwamishinan ya nuna damuwa game da yadda ake amfani da harabar makarantu ba bisa ka’ida ba, musamman yadda wasu mazauna yankunan suka mayar da harabar Makarantar Murtala Muhammad wajen zubar da shara.
Ya tabbatar da cewa za a ɗauki matakin gaggawa don dakile lalacewar muhalli da kuma tabbatar da amintaccen wuri don karatu.

Yayin zagayen nasa, Dr. Makoda ya kuma kai ziyara zuwa Makarantar Sakandare ta ‘Yan Mata da ke Guringawa, inda ya duba aikin gine-gine da gyare-gyare da ke gudana.
Ya yaba da jajircewar ɗan kwangilar wajen cika aikin cikin lokaci da kuma bin ƙa’idojin aikin.
Aikin ya haɗa da gine-ginen bene biyu masu ɗakunan karatu huɗu kowanne, bandakunan ɗalibai da na malamai, da ofisoshin malamai, da gina katangar makarantar da kuma rijiyar burtsatse don samun ruwan sha mai tsafta.
Kwamishinan ya kuma kai ziyara zuwa Makarantar Sakandare ta Tukun Tawa, wacce aka gyara a baya ƙarƙashin shirin 484 Ward Project na jihar, wanda ke karkashin jagorancin ƙananan hukumomi. Ya bayyana wannan a matsayin misali na ci gaba daga matakin ƙasa a fannin ilimi.
Ya jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf yana nan daram da alkawarin da ya ɗauka na samar da ingantaccen ilimi ga kowanne yaro a Jihar Kano.
Idan za a iya tunawa, a baya Gwamnatin Kano ta amince da kashe biliyoyin naira domin sauya fasalin ilimi da inganta gine-ginen makarantu.
Khadijah Aliyu
-
Labarai5 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai6 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai6 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai6 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
-
Labarai3 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
