Labarai
Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Ta Jinjinawa Gwamnan Kano Bisa Ayyukan Cigaban Jihar
Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed, ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa kokarinsa wajen inganta ci gaban zamantakewar al’umma da kuma tallafawa aiwatar da Muradun Cigaba mai Dorewa (SDGs).
Hajiya Amina Mohammed ta kai ziyara Jihar Kano ne domin yin ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar bisa rasuwar fitattun dattawan nan biyu, wato Alhaji Aminu Alhassan Dantata da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
A yayin ziyarar tata, Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniyar ta nuna gamsuwa da wasu daga cikin shirye-shiryen Gwamna Yusuf na cigaban al’umma, musamman wadanda suka yi daidai da muradun ci gaban duniya.
Daga cikin wadannan shirye-shirye akwai sanya fitilu masu amfani da hasken rana a titunan Kano, kafa cibiyar kula da cututtuka ta Kano (Kano Centre for Disease Control), wadda ita ce irinta ta farko da wata gwamnati ta jiha ta kafa a Najeriya, da kuma kokarin fadada tsarin inshorar lafiya domin al’ummar jihar su amfana.
Ta kuma yaba da kirkirar Ma’aikatar Wutar Lantarki da Makamashi, tare da sake tsara Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi, wanda dukkansu ke nuni da jajircewar gwamnati wajen daukar matakan kare muhalli da dorewar ci gaba.
Hajiya Mohammed ta bayyana cewa ziyarar tata ba wai kawai domin ta’aziyya ba ce, har da zurfafa wayar da kai kan Muradun Ci Gaba Mai Dorewa, da kuma karfafa hadin gwiwa da jihar Kano.
Ta sanar da gwamnan game da babban taron Kasuwanci da Zuba Jari na Majalisar Dinkin Duniya da ke tafe, tare da nuna godiya bisa dagewarsa wajen karfafa mata, samar da ayyukan yi, da kare muhalli.
A nasa jawabin , Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa a shirye jiharsa take ta hada gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya musamman a fannonin ilimi, lafiya, sauyin yanayi, samar da makamashi, kare muhalli da kuma zuba jari mai dorewa.
Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da manufofin ci gaba da za su inganta rayuwar al’ummar Kano da kuma bada gudunmawa ga kokarin ci gaban duniya.
Abdullahi Jalaluddeen
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
