Labarai
Kashim Shettina Ya Ziyarci Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Da Sarkin Daura
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettina ya ce gwamnatin tarayya za ta samar da sabbin dabarun yaki da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da sauran kalubalen tsaro da ake fuskanta a sassan kasar nan.
Mataimakin shugaban kasa Shettina ya bayyana haka ne bayan ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidan sa dake Daura.
Shettima ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya za ta kuma kara samar da kayan aiki da kwararrun da ake bukata domin dawo da tsaro da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta kuduri aniyar cika alkawuran da ta dauka ga ‘yan Najeriya a yakin neman zabe, duk da kalubalen da ake fuskanta na tattalin arziki, yayin da ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da marawa gwamnatin baya da kuma taya ta da addu’a.
Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu rakiyar ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki Sanata Atiku Bagudu da ministan noma da samar da abinci Alhaji Abubakar Kyari da kuma tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha, sun kuma kai gaisuwar ban girma ga Mai Martaba Sarkin Daura. , Alhaji Umar Faruk Umar a fadar sa dake Daura.
Daga Isma’il Adamu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
