Labarai
Jihar Jigawa Za Ta Kafa Asusun Bada Agaji Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta kafa asusun bada agajin gaggawa na dindindin domin kula da Iftila’in ambaliyar ruwa da ke faruwa a jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan jihar Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa manema labarai a Dutse.
Ya ce gwamna Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da kwamitin kula da Iftila’in ambaliyar ruwa a gidan gwamnati na Dutse.
A cewarsa, kwamitin wanda Architect Aminu Kani ke jagoranta, yana da alhakin kammala kafa asusun bada agajin gaggawa na ambaliya.
Hamisu Gumel ya ci gaba da bayanin cewa, an dora wa ‘yan kwamitin alhakin gudanar da ayyukansu cikin sauki da kuma tafiyar da asusun.
A jawabinsa yayin kaddamarwar, Gwamna Namadi ya bayyana jin dadinsa da irin ci gaban da aka samu kawo yanzu wajen magance matsalar ambaliyar ruwa a shekarar 2022.
Ya kuma jaddada muhimmancin daukar matakin gaggawa wajen magance matsalolin da ke kan gaba a cikin rahoton kwamitin da ya gabata.
Ya yaba da kokarin da tsohon kwamatin ya yi, wanda ya tattara sama da naira biliyan 1 da aka ware domin samar da tallafi ga sama da mutane dubu talatin da hudu da Iftila’in ya shafa.
“Manufar ita ce Asusun Tallafawa ya zama matakin gaggawa na farko don gyarawa da kuma bada agaji ga wadanda iftila’in ya rutsa da su a kan tsari mai dorewa. Tuni tsohon kwamitin ya gabatar da wani daftarin kudirin doka amma yana bukatar a sake duba shi kafin a kammala shi domin daukar matakin da ya dace.” Inji shi.
Ya ce Gwamna Namadi ya bayyana kwarin gwiwa kan yadda mambobin kwamitin za su iya cika aikinsu a cikin wa’adin watanni biyu.
Ya kuma kara da cewa Gwamnan ya ba su tabbacin tallafin kayan aiki da suka dace don saukaka gudanar da ayyukansu cikin sauki.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
