Ilimi
Auren Wuri Babbar Matsala Ce Ga Arewacin Nijeriya – Hauwa

An bayyana matsalar auren wuri ga ‘ya’ya mata musamman a yankin Arewacin Nijeriya a matsayin wata hanya dake haifar da koma baya ga ci gaba da tattalin arzikin yankin.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban makarantar sakandaren gwamnatin tarayya ta mata ( ABULOMA ) Hajiya Hauwa Abubakar Yamusa ta bayyana hakan, lokacin da take ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron bikin cikar makarantar shekaru 50 da kafuwa, wanda ya gudana a gidan Tarihi na Arewa dake Kaduna.
Shugabar makarantar ta ƙara da cewar, babbar matsalar dake haifar da matsala a Arewa yana da alaƙa da matsalar auren wuri da ake yi wa yara mata, tauye yara Mata daga samun ilimi da tursasa musu aure suna ƙananan shekaru matsala ce babba.
“A har kullum ina bayar da misali ga kaina, mahaifina ya sa ni makarantar Boko, ya kuma yi tsayuwar daka wajen ganin na samu cin gajiyar karatun, wanda hakan ne ya zama sila wanda a yanzu nake matsayin da nake ciki na jagorancin wannan makaranta tare da shirya wannan muhimmin taro “
Daga ƙarshe Hajiya Hauwa Abubakar Yamusa ta yi kira ga iyaye da Malaman addini da su bayar da tasu gudummawar domin samun wannan nasara da ake nema
Shettima A.
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
