Labarai
Gwamnatin Zamfara Ta Ayana Dokar Ta-baci Kan Shan-Inna a Karamar Hukumar Gummi
Gwamnatin Jihar Zamfara ta ayyana dokar ta-baci kan cutar shan-inna a Karamar Hukumar Gummi domin dakile yaduwar cutar da kuma kara karfafa ayyukan rigakafi.
Kwamishinar Lafiya ta jihar, Dakta Nafisa Muhammad Maradun, ta bayyana hakan a taron wata-wata na kwamitin kula da harkokin kiwon lafiya na matakin farko da aka gudanar a ofishin Mataimakin Gwamnan jihar a Gusau.
Ta ce matakin zai taimaka wajen kara sa ido kan cutar, fadada shirin allurar rigakafi da kuma wayar da kan al’umma domin hana yaduwar ta.
Mataimakin Gwamnan jihar, Mani Mallam Mummuni, ya jaddada muhimmancin allurar rigakafi wajen kare lafiyar jama’a musamman yara.
Ya kuma bayyana cewa a watan Maris za a gudanar da gangamin allurar rigakafin shan-inna wanda ake sa ran zai kai ga sama da yara miliyan daya da dubu dari uku a fadin jihar.
Haka kuma ya bukaci hukumomin lafiya su tabbatar da cewa alluran sun isa ga yaran da aka tsara su karba.
Shi ma mai kula da ayyukan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a jihar, Dakta Raji Mukhtar, ya tabbatar da cewa za su ci gaba da bai wa gwamnatin Zamfara goyon baya wajen kawo karshen cutar shan-inna.
Aminu Dalhatu/Gusau
-
Labarai7 days agoAna Zargin Mutum 140 Sun Bace Bayan Nutsewar Jirgin Ruwan Iran a Gaɓar Sri Lanka
-
Labarai7 days agoJam’iyyar APC Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni a Jihar Kano
-
Labarai6 days agoRamadan: Sarkin Kauru Ya Bukaci a Kara Karfafa Tsaro Tare da Tallafawa Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Miliyoyin Naira Don Sayen Gidaje 96 Daga Gwamnatin Tarayya
-
Labarai5 days agoKaramar Hukumar Birnin Kudu ta Nemi Hadin Kan Kungiyar ‘Yan Achaba Wajen Dakile Matsalar Tsaro
-
Labarai5 days agoSojojin Najeriya Sun Karɓi Motocin Yakin Da Aka Kera A Cikin Ƙasa
-
Ilimi7 days agoGwamnatin Tarayya da ke Gusau za ta Kafa Cibiyar Nazari kan Tarihi da Al’adun Zamfara
-
Labarai5 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kano Ta Fara Shari’ar Tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam
