Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jigawa ta Baiwa Kungiyar Tsoffin Sojoji Gagarumar Gudummawa

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Kungiyar Tsoffin Sojoji reshen jihar Jigawa ta samu tallafin sama da naira miliyan 40 a wajen taron kaddamar da Gidauniyar Tallafawa Kungiyar na bana, wanda aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana matuƙar godiyarsa ga irin sadaukarwar da mambobin Legion suka yi, ciki har da waɗanda suka sadaukar da rayukansu wajen hidimtawa ƙasa.

Ya jaddada cewa irin wannan sadaukarwa za ta ci gaba da kasancewa a tarihin ƙasa, tare da tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Jigawa da al’ummar jihar za su ci gaba da nuna godiya da tallafa wa tsoffin sojojin domin samun ingantacciyar rayuwa.

Gwamna Namadi ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 10 daga gwamnatin jihar, tare da tasa gudummawar ta Naira miliyan 2. Mataimakin Gwamna, Injiniya Aminu Usman, shi ma ya bayar da Naira miliyan 2, yayin da ƙananan hukumomi 27 na jihar suka bayar da gudummawar haɗin gwiwa ta Naira miliyan 13.

Sauran manyan gudummawa sun haɗa da na mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar, Shugaban Ma’aikatan Gwamnati (Head of Service), Manyan Mataimaka da Masu Ba Gwamna Shawara na Musamman, shugabannin hukumomin tsaro, da kuma Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Correspondents’ Chapel, wadda ta bayar da Naira dubu 100.

A  jawabin, Shugaban Kungiyar Tsoffin Sojojin Nijeriya a Jihar Jigawa, Malam Aliyu Mustapha, ya gode wa gwamnatin jihar da al’ummar jihar baki ɗaya bisa ƙauna, tausayi da girmamawa da suke nuna wa mambobin Legion.

Ya bayyana cewa irin wannan kyakkyawar mu’amala tana ƙara ƙarfafa gwiwar kowa a cikin al’umma, tare da nuna cewa ba a manta da sadaukarwar da suka yi a baya ba.

Ga ’yan uwana tsoffin sojoji, ina tabbatar muku da cewa Gwamnatin Jihar Jigawa na tsaye daram tare da mu,” in ji Shugaban.

Ina matuƙar jin daɗin wannan karamci, kuma ina sake tabbatar da kudurin Kungiyar Tsoffin Sojojin Najeriya na ci gaba da fafutuka da hulɗa tare domin inganta walwalar dukkan mambobin Legion a faɗin jihar.”

 

 

Labarai

Labarai16 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai18 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai7 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara