Connect with us

Labarai

‘Yan Sanda Sun Bankado Maboyar Masu Garkuwa

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta samu wani gagarumin nasara a kokarinta na yaki da masu garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka a jihar.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Ramhan Nansel, ya fitar, ya ce jami’an Sashen Leken Asiri na Jihar (SID) sun samu sahihan bayanai da suka kai su ga bankado maboyar wani fitaccen mai garkuwa da mutane a Gidan Akuya da ke karamar hukumar Keana ta jihar.

Sanarwar ta ce da zarar masu laifin suka hango jami’an tsaro, sai suka yi kokarin tserewa daga wurin, amma ‘yan sanda suka bi su da sawu inda a yayin samamen aka samu nasarar kama wani da ake zargi mai suna Jibril Yunusa.

Binciken da aka gudanar a maboyar ya kai ga kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, mujallar harsashi daya mara komai, da kuma bindiga kirar gida guda daya.

A cewar sanarwar, yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya shiga cikin hare-haren garkuwa da mutane da dama a yankunan Keana da Awe na jihar, tare da bayar da wasu muhimman bayanai da za su taimaka wajen ci gaba da bincike.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Shetima Jauro Mohammed, ya umarci jami’an rundunar da su kara zage damtse domin kamo sauran ‘yan kungiyar da suka tsere.

Ya kuma tabbatar wa mazauna jihar kudurin rundunar na ci gaba da yaki da laifuka tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a ko’ina cikin jihar.

Aliyu Muraki/Lafia

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara