Labarai
Gwamnatin Zamfara Ta Amince da Biyan Albashin Watan Maris Gabanin Bukukuwan Karamar Sallah
Daga Aminu Dalhatu
Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da biyan albashin watan Maris da wuri ga dukkan ma’aikatan gwamnati da masu karɓar fansho a faɗin jihar, gabanin bikin Sallar Eid-el-Fitr.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu, Mahmud Muhammad Dantawasa ya fitar, ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin saukaka wa ma’aikata da wadanda suka yi ritaya, tare da ba su damar yin shirye-shiryen Sallah yadda ya kamata.
Dantawasa ya bayyana cewa, bisa ga bayanin da aka samu daga Ofishin Akanta Janar na Jihar, an kammala dukkan shirye-shirye da suka dace domin tabbatar da an biya albashi da fansho cikin gaggawa ga dukkan waɗanda suka cancanta a faɗin jihar.
Ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na ci gaba da kula da jin daɗin ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho, tare da yaba musu bisa sadaukarwa da gudummawar da suke bayarwa wajen ci gaban Jihar Zamfara.
Mahmud Dantawasa ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ba da fifiko ga manufofin da za su inganta rayuwar ma’aikata da wadanda suka yi ritaya.
Haka kuma ya buƙaci ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho da su ci gaba da mara wa manufofin gwamnati baya, tare da yin addu’ar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa a Jihar Zamfara.
Gwamnatin Jihar Zamfara ta kuma yi wa dukkan ma’aikatan gwamnati, da wadanda suka yi ritaya, da kuma al’ummar jihar fatan yin Sallar Eid-el-Fitr cikin kwanciyar hankali da farin ciki.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
