Labarai
Shugaba Tinubu Ya Amince da Sake Kafa Kwamitin Hukumar Kula da Wutar Lantarki
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sake kafa Kwamitin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC), bayan Majalisar Dattawa ta tabbatar da mambobin kwamitin a ranar 16 ga Disamba.
Mambobin sabon kwamitin sun haɗa da: Mulisiu Olalekan Oseni a matsayin Shugaba, da Yusuf Ali a matsayin Mataimakin Shugaba.
Sauran mambobin sun hada da Mista Nathan Rogers Shatti Kwamishina, Mista Dafe Akpeneye Kwamishina, Aisha Mahmud Kanti Bello Kwamishina, Dokta Chidi Ike Kwamishina, da Dokta Fouad Animashaun Kwamishina.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga mambobin kwamitin NERC da su zurfafa tare da ƙarfafa sauye-sauyen da ake yi a ɓangaren wutar lantarki na Nijeriya, bisa bin doka da dokar Wutar Lantarki ta 2023.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
