Labarai
Shugaban Majalisar Dattawa Akpabio ya Nemi Sanata Natasha ta Biya Shi Diyyar Biliyan 200
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya shigar da Sanata Natasha Akpoti ƙara a kotu kan zargin ɓata masa suna yana mai neman ta biya shi diyyar naira biliyan 200.
Sanata Natasha mai wakiltar jihar Kogi ta tabbatar da karɓar sammacin a shafukanta na sada zumunta, inda ta nuna jin daɗinta tana mai cewa ta samu damar bayyana hujjojinta kan zargin yunƙurin lalata da ta zarge shi da yi a baya.
“Na yi farin ciki da Sanata Akpabio ya taso da wannan batu saboda kwamatin ɗa’a na majalisa ya ƙi amincewa ya saurare ni kan batun sakamakon matar Akpabio ta shigar da ni ƙara a kotu.”
A watan Fabrairun 2025 ne Natasha ta zargi Akpabio da neman yin lalata da ita bayan rikicin da ya ɓarke a tsakaninsu, wanda ya kai ga dakatar da ita daga zaman majalisar na tsawon wata shida.
-
Labarai6 days agoGwamnatin Kebbi Ta Bukaci Malamai Su Yi Wa’azin Zaman Lafiya
-
Labarai6 days agoSojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 45 a Katsina
-
Labarai6 days agoRanar Mata Ta Duniya: Gwamnatin Kano Ta Bukaci A Kara Tallafa wa Mata da ’Yan Mata
-
Labarai4 days agoAn Nada Kabir Yahaya Darakta Janar na Farko na Filin Jirgin Sama da ke Gusau
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Biyu Da Ake Zargin ’Yan Bindiga Ne a Kwara
-
Labarai6 days agoNCAA ta Yaba wa Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi Bisa Kyakkyawan Tanadin Aikin Hajji
-
Labarai6 days ago’Yan Sanda Sun Kama Mutane Biyu Kan Lalata Kayan Wutar Lantarki a Nasarawa
-
Labarai4 days agoKwastam ta Kama Kayayyaki na Sama da Naira Miliyan 478 a Jihar Kwara
