Labarai
Majalisar Kaduna Ta Amince da Dokar Kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani
Daga Shamsuddeen Mannir Atiku
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokar kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani ta Jihar Kaduna, wacce za ta taimaka wajen ƙarfafa tsarin fasaha na jihar da inganta gasa a fannin tattalin arziki.
Dokar mai taken “Kaduna State Information Technology and Digital Economy Agency and for Related Matters, 2025” ta samu amincewa bayan karatu na uku a zaman majalisar na ranar Talata.
Shugaban majalisar, Hon. Yusuf Dahiru Liman, wanda ya jagoranci zaman, ya bayyana muhimmancin dokar, yana mai cewa kafa hukumar zai faɗaɗa damar tattalin arziki tare da bai wa jihar Kaduna damar cin moriyar cigaban fasahar zamani a duniya.
Ya ce hukumar za ta ƙarfafa kirkire-kirkire, bunƙasa ƙwarewar dijital, da daidaita jihar da sauye-sauyen fasaha da tattalin arzikin dijital a duniya.

Tun da farko, shugaban kwamitin haɗin gwiwa kan Yada Labarai, Kungiyoyi Masu Zaman Kansu da Abokan Cigaba, Mr. Henry Marah Zakariah, ya gabatar da rahoton kwamitin.
Ya bayyana cewa an yi nazari mai zurfi kan dokar, kuma an tabbatar da cewa mataki ne mai muhimmanci wajen ƙara damar samun ayyukan yi da sauƙaƙa wa al’umma samun ilimin fasahar zamani.
Mr. Henry Zakariah ya kuma jaddada cewa kafa hukumar za ta bunƙasa tattalin arzikin jihar da samar da kudaden shiga, inda ya bayyana cewa za a kafa cibiyoyin fasahar zamanin a yankunan karkara domin bai wa kowa damar cin gajiyar ayyukan Hukumar.
Daga karshe majalisar ta amince da dokar baki ɗaya, bayan Dan Majalisa mai wakiltar mazabar Birnin Zaria, Barr. Mahmood Lawal Sama’ila ya gabatar da kudirin amincewa inda ya samu goyon baya daga Dan Majalisa mai wakiltar mazabar Makarfi, Isiyaku Ibrahim ya goyi bayan shi.
-
Labarai7 days agoSojojin Najeriya Sun Karɓi Motocin Yakin Da Aka Kera A Cikin Ƙasa
-
Labarai7 days agoKaramar Hukumar Birnin Kudu ta Nemi Hadin Kan Kungiyar ‘Yan Achaba Wajen Dakile Matsalar Tsaro
-
Labarai4 days agoRanar Mata Ta Duniya: Gwamnatin Kano Ta Bukaci A Kara Tallafa wa Mata da ’Yan Mata
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kano Ta Fara Shari’ar Tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam
-
Labarai4 days agoGwamnatin Kebbi Ta Bukaci Malamai Su Yi Wa’azin Zaman Lafiya
-
Labarai4 days agoSojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 45 a Katsina
-
Labarai6 days agoRamadan: Tinubu Ya Kara Jaddada Kudirinsa na Inganta Rayuwar Jami’an Soji
-
Labarai7 days agoTsarin Kundin Shirin Bunkasa Samarda Abinci Mai Gina Jiki
