Ilimi
Ma’aikatan Da Ba Malamai Ba A Jami’ar Jihar Taraba Sun Fada Yajin Aiki
Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU), Comr. Muhammad Haruna Ibrahim ya bukaci gwamnatin jihar Taraba da ta gaggauta biyan ‘yan kungiyar SSANU, jami’ar Jalingo ta jihar Taraba alawus-alawus da suke bi bashi.
Comr. Haruna ya yi wannan bukata ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron majalisar zartarwa na shiyyar karo na 11 da ya gudana a Jalingo.
Shugaban SSANU ya dage cewa ya kamata a yi wa ’ya’yan kungiyar adalci, domin wadanda ba aikin koyarwa ba na daga cikin bangarori hudu da suka kafa jami’a.
Sai dai ya yi gargadin cewa kungiyar ba za ta goyi bayan duk wani memba da ya sabawa ka’idojin jami’a ba.
Tun da farko, Comr. Bitrus Joseph Ajibauka, shugaban kungiyar TSU reshen, ya yabawa gwamna Agbu Kefas bisa yadda ya amince da biyan wani bangare na bashin albashi da alawus-alawus na kungiyar da kuma aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000.
JAMILA ABBA
-
Labarai5 days agoRanar Mata Ta Duniya: Gwamnatin Kano Ta Bukaci A Kara Tallafa wa Mata da ’Yan Mata
-
Labarai5 days agoGwamnatin Kebbi Ta Bukaci Malamai Su Yi Wa’azin Zaman Lafiya
-
Labarai5 days agoSojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 45 a Katsina
-
Labarai7 days agoGwamnatin Zamfara Ta Ayana Dokar Ta-baci Kan Shan-Inna a Karamar Hukumar Gummi
-
Labarai5 days agoNCAA ta Yaba wa Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi Bisa Kyakkyawan Tanadin Aikin Hajji
-
Labarai5 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Biyu Da Ake Zargin ’Yan Bindiga Ne a Kwara
-
Labarai3 days agoAn Nada Kabir Yahaya Darakta Janar na Farko na Filin Jirgin Sama da ke Gusau
-
Labarai5 days ago’Yan Sanda Sun Kama Mutane Biyu Kan Lalata Kayan Wutar Lantarki a Nasarawa
