Kasuwanci
Gwamnan Jigawa Ya Halarci Taron Ranar Ma’aikata Ta Bana
Gwamna Umar Namadi ya bi sahun kungiyoyin kwadago domin tunawa da irin gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa wajen ci gaban jihar Jigawa.
Da yake gabatar da jawabinsa, Gwamna Namadi ya yaba da jajircewar ma’aikatan Jigawa, inda ya bayyana ma’aikata a matsayin masu kawo ci gaba.
Ya bayyana cewa, ma’aikata a dukkan bangarori suna aiki da gaske a matsayin injin da ke ba da kuzarin motsa al’umma zuwa ga ci gaba.
Ya kuma kara jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da walwalar ma’aikata, inda ya bayar da misali da nasarorin da aka samu da suka hada da aiwatar da mafi karancin albashi na Naira 70,000, gina gidaje masu saukin kudi ga ma’aikatan gwamnati, da kuma shigar da sama da Naira biliyan 7 a cikin shirin bayar da gudunmawar fansho na jihar.
Gwamnan ya karkare da sako mai ratsa jiki ga ma’aikata, yana mai cewa, “Watakila ba za ku ji dadin aikinku dari bisa dari ba, amma ina tabbatar muku, guminku ba zai tafi a banza ba.
Kwamared Sunusi Alhassan Maigatari, wanda ya yi magana a madadin kungiyar kwadagon, ya amince da wannan ci gaba, inda ya bayyana Gwamna Namadi a matsayin gwamnan al’umma.
Ya kuma yabawa ajandar gwamnati mai dauke da abubuwa 12, wadanda suka samar da fa’idodi masu inganci da suka hada da daukar dimbin ma’aikata a sassa masu muhimmanci, shirin ba da lamuni na noma ga ma’aikata, da kafa shagunan dake sayarda kaya da rahusa domin dakile matsalolin tattalin arziki.
USMAN MZ/Dutse
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
