Labarai
Gwamna Uba Sani Ya Nada Sarkin Kauru Amirul Hajj Na Shekarar 2025
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya naɗa Sarkin Kauru, Mai Martaba Alhaji Ya’u Shehu Usman, a matsayin Amirul Hajj kuma jagoran tawagar jami’an jihar don aikin Hajjin 2025.
A cikin wata sanarwa, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Ibraheem Musa, ya bayyana cewa naɗin wannan basarake mai daraja ya biyo bayan sadaukarwarsa, da gaskiya, da jagorancinsa, da nagarta a harkokin mulki.

A matsayinsa na Amirul Hajj, Sarkin zai yi aiki kafada da kafada da Kwamitin Hajj na Musamman na Jihar Kaduna tare da haɗin gwiwa da hukumomin Jiha, Tarayya, da na ƙasashen duniya, domin tabbatar da aikin Hajji cikin nasara ga maniyyatan Jihar Kaduna.
Gwamnan ya kuma yi addu’a ga Allah da ya ma Sarkin jagora da kariya yayin gudanar da wannan muhimmin aiki.
Safiyah Abdulkadir
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
