Labarai
NUJ Ta Bada Tallafin Azumi Ga Iyalan Mambobinta Da Suka Rasu A Jihar Kebbi

Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kebbi ta raba kayan abinci da kudi ga iyalan mambobinta da suka rasu a lokacin da suke kan aikin jarida, a matsayin kyautar azumin Ramadan.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kungiyar na Jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar, ya ce suna gudanar da wannan shiri a duk shekara, tun bayan kaddamar da shi da tsohon shugaban kungiyar na jiha Alhaji Aliyu Jajirma ya yi, domin faranta ran iyalan abokan aikinsu da suka rasu.
Kwamared Sarki Abubakar ya bayyana cewa dukkan shugabannin kungiyar da suka gabata sun tabbatar da ci gaba da gudanar da wannan shiri a duk lokacin azumin Ramadan domin rage wa iyalan mamatan radadin wahalhalun rayu.
Ya sanar da cewa kowane iyali daga cikin iyalan mambobi 21 da suka rasu za su karɓi buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 25 da kuma naira dubu goma.
Yayin da yake gode wa Gwamnatin Jihar Kebbi karkashin jagorancin Kwamared Nasiru Idris saboda goyon bayan da take bai wa kungiyar, Kwamared Sarki ya yaba da ayyukan ci gaba da Gwamna Nasir Idris ya aiwatar a cikin shekaru biyu da suka gabata domin inganta rayuwar al’ummar jihar.
Kwamishinan Watsa Labarai da Al’adu na Jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Ahmed BK, yayin da yake yaba wa shugabancin kungiyar saboda tallafin da ta bai wa iyalan mamatan, ya tabbatar wa kungiyar cewa Gwamnatin jihar za ta ci gaba da fifita jin daɗin ‘yan jarida a jihar.
Haka kuma, ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa badi an gudanar da wannan taro cikin gagarumin shiri domin faranta wa iyalan mamatan rai.
A madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, daya daga cikin matan wadanda suka rasu, Hajiya Hadiza Abdullahi, ta gode wa kungiyar saboda tunawa da su bayan rasuwar mazajensu.
Daga Abdullahi Tukur
-
Labarai4 days ago
Al’ummar Babura Sun Karrama Sabon Shugaban Asibitin Koyarwa Na Rasheed Shekoni
-
Labarai6 days ago
Gwamna Namadi Ya Bada Aikin hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
-
Ilimi5 days ago
Tsangayar Ilimi Ta BUK Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
-
Ilimi3 days ago
An Fara Bada Horo Ga Masu Horas da Maniyatan Bana A Jigawa
-
Kasuwanci2 days ago
Hukumar NSCDC ta tura jami’an tsaro 415 domin aikin Easter a Zamfara.
-
Labarai4 days ago
KADGIS Za Ta Yi Amfani Da Sabuwar Manhajar Biyan Diyyar Filaye A Kaduna
-
Labarai7 days ago
Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
-
Labarai3 days ago
Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Shirya Bitar Ga Malaman Bita na Kananan Hukumomi 27