Labarai
‘Yan Sanda Sun Mika Bakin Haure 165 Ga Hukumar Shige Da Fice Ta Kasa
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kebbi, ta kama wasu bakin haure 165 tare da mika su ga hukumar kula da shige da fice ta kasa shiyar jihar domin gudanar da bincike.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar ya fitar kuma ya mikawa gidan rediyon Najeriya a jihar Kebbi, ya ce, bisa rahoton bayanan sirri, an gano sama da mutum dari biyu a wani katafaren gida mai dakuna uku da ke unguwar Kuwait a cikin birnin Birnin Kebbi.

Sanarwar ta ce, tawagar jami’an ‘yan sanda da ke sashin binciken manyan laifuka (SCID) ce ta kai samame unguwar, inda suka yi nasarar cafke mutane dari da sittin da biyar (165).

Ya bayyana cewa, yayin da ake gudanar da bincike, an gano cewa, dukkan wadanda ake zargin sun fito ne daga kasashen Faransa da suka hada da Burkina Faso, da Jamhuriyar Benin, da Jamhuriyar Nijar, da Mali da Ivory Coast.

A cewar sanarwar, bincike ya kara nuna cewa, wadanda ake zargin suna zaune ne a Najeriya ba tare da wasu takardu masu inganci ba.
Sanarwar ta ce, bayan kammala binciken farko da rundunar ta gudanar, an mika wadanda ake zargin zuwa hukumar kula da shige da fice ta kasa shiyyar jihar Kebbi, domin ci gaba da bincike da kuma daukar matakin da ya dace.
Daga Abdullahi Tukur
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai2 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai4 hours agoAKCILS Ta Karrama Jami’in Tsaro Bayan Shekaru 22
-
Labarai2 days ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
