Connect with us

Labarai

Masu Fama Da Cutar Daji Sun Bukaci Gwamnatin Kano Basu Tallafi

Published

on

Kungiyar masu fama da cutar daji ta Najeriya reshen jihar Kano, ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta bullo da tallafin kula da cutar a dukkan asibitocin gwamnati.

Shugaban kungiyar Salisu Yusuf ne ya yi wannan kira a yayin wani taron manema labarai na bikin ranar cutar Daji ta duniya tta shekarar 025.

Ya bukaci gwamnati da ta hada gwajin cutar Kansa, da jiyya, da kula da lafiyar jiki a cikin shirinta na ba da tallafin iwon lafiya.

Acewarsa matakin zai rage wa majinyata matsalar kudi, musamman wadanda suka fito daga iyalai masu karamin karfi.

Bugu da kari, kungiyar ta bukaci da a saka masu fama da cutar ta Daji da wadanda suka warke daga cutar a cikin shirin nan na Abba Care da aka kaddamar kwanan nan, wanda ke da nufin tallafa wa mutane masu raunu su 300,000.

Salisu Yusuf ya jaddada cewa cutar Kansa ta kasance babbar lalurar da ke bukatar kulawa cikin gaggawa. “Yawancin mutane na kokawa dangane da biyan kuɗin tantance masu dauke da cutar, da kudaden cigaba da samun kula da karbar magani idan aka gano suna dauke da cutar.

Kungiyar ta masu fama da cutar daji ta Najeriya ta yabawa kokarin gwamnatin jihar na inganta fannin kiwon lafiya, tare da yin kira ga masu hannu da shuni, da kungiyoyi masu zaman kansu, da  cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu, da su tallafawa shirin kula da cutar Daji a Kano.

Ta  jaddada kudirinta na bayar da shawarwarin sauye-sauyen tsarin da ke ba masu fama da cutar Kansa fifiko a Kano, ta hanyar wayar da kan jama’a da shirye-shiryen gano cutar da wuri.

Taken ranar Ciwon Daji ta Duniya na 2025, “United by Unique,” yana nuna mahimmancin aikin gamayya wajen yaƙar cutar Kansa.

Abdullahi Jalaluddeen

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara