Labarai
An Kara Wa’adin Yin Rajistan Aikin Hajjin 2025
Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta sanar da a ci gaba da yi wa maniyyata rajista har zuwa ranar Litinin 10 ga watan Fabrairu, 2025.
A daren Talata 4 ga watan ne hukumar ta amince da kara lokacin a taron da ta yi da shugabannin hukumomin alhazai na jihohi.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Jin Dadin Alhazzai ta Jihar Kaduna Yunusa Mohammed Abdullahi ya fitar, ya ce shugaban hukumar Malam Salihu S. Abubakar ya yi kira ga maniyyatan jihar ta Kaduna da su yi amfani da wannan damar wajen yin rajista ta hanyar tuntubar jami’anmu da ke kananan hukumomi don su cika kudadensu, ko karbar sabuwar telar banki don su biya kafin a rufe.
Ya ce wannan ita ce dama ta ƙarshe da suka nema a wajen taron da suka yi da NAHCON.
Kudin kujera a bana dai ya kama Naira miliyan takwas da dubu dari hudu da hamsin da biyar, da dari shida da tamanin da biyar, da kobo hamsin da tara(8, 457, 685.59).
Safiyah Abdulkadir
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
