Labarai
Shugaba Tinubu Ya Dawo Daga Bikin Rantsar Da Sabon Shugaban Ghana
Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja daga birnin Accra na kasar Ghana, inda ya shaida bikin rantsar da sabon shugaban kasar John Dramani Mahama.
A wajen taron, Shugaba Tinubu ya nemi hadin kan Nahiyar, inda ya kara da cewa, zai yi aiki tare da sabon shugaban kasar Ghana, domin samun nasarar kasashen biyu.
Shugaba Tinubu ya ba da tabbacin cewa kasashen Afirka ‘yan uwan juna ne, ba za su cutar da juna ba ko da sun shiga cikin rudani na rashin jituwa.
Shugaban kara da cewa, ba za su taba cutar da junansu ba kuma ba za su bari wani bare ya cutar da su ko kuma kawo cikas ga hadin kan su ba.
Ya ce idan aka mayar da hankali a kai, kungiyar raya tattalin kasashen Afirka na yamma ECOWAS za ta iya magance matsalolin da ke addabar yankin da suka hada da fatara,da rashin aikin yi ga matasa, da rashin zaman lafiya, da tada kayar baya, da sauran matsalolin da ke kawo cikas ga ci gaban da ake bukata.
Shugaba Tinubu ya yi hutun Kirsimeti ne a Legas, ya kuma kaddamar da wasu ayyuka a jihar Anambra kafin ya bar Legas zuwa Ghana domin bikin rantsar da sabon shugaban Ghana, John Dramani Mahama.
Daga Bello Wakili
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
